1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban na korofi kan MDD

Usman Shehu Usman
May 2, 2023

Gwamnatin Afghanistan ta garadi MDD kan tattauna matsalar karsa ba tare da ita ba. Shugaban ofishin siyasa na Taliban a Doha, Suhail Shaheen ya ce "Duk wani taro ba tare da halartar mahukuntan Kabul ba

https://p.dw.com/p/4QnwU
Afghanistan Taliban-Vertreter führen in Doha Gespräche mit US-amerikanischen und europäischen Delegierten
Hoto: Stringer/REUTERS

Gwamnatin Afghanistan ta garadi MDD kan tattauna matsalar karsa ba tare da ita ba. Shugaban ofishin siyasa na Taliban a Doha, Suhail Shaheen ya ce "Duk wani taro ba tare da halartar wakilan Daular Musuluncin Afganistan ba IEA (wato hukumomin Afganistan), toh ba zai haifar da da mai ido ba, kuma zai zama aikin banza. Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya shirya tattaunawar karo na biyu a Doha babban birnin kasar Katar, bayan da gwamnatin Taliban ta haramta wa matan Afghanistan aiki da Majalisar Dinkin Duniya, lamarin da ya sa hukumar ta duniya ta sanya ido matuka kan ayyukan agajin da take gudanarwa a Afghanistan. Tattaunawar ta kunshi wakilai daga Amirka da Rasha da China da kuma wasu kasashe da kungiyoyi 20 da suka hada da manyan kasashen Turai masu ba da taimako da makwabta Afganistan irin su Pakistan, amma ba a hada da gwamnatin Taliban ba. Don haka gwamnatin Afganistan ke cewa ta yaya za a amince da shawarar da aka yanke a irin wadannan tarurrukan ko kuma a aiwatar da su alhali ba mu cikin tsarin? Yana nuna wariya da rashin adalci.