Talafa wa marasa galhu a Najeriya | Himma dai Matasa | DW | 04.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Talafa wa marasa galhu a Najeriya

A Jihar Katsina ta Najeriya an girka wata kungiya mai taimakon al'umma marasa galihu.

Kungiyar wacce ake kira da sunan Arewa Less Previllage a turance  ta dauki nauyin yi wa mutane fiye da 700 aikin ido kyauta a fadin jihar ta katsina.Ita dai wannan kungiya ita ce ke biyan kudaden da ake yi wa al,umma gyaran ido kyauta a asibitin ido na tsohuwar kasuwa da ke cikin garin Katsina.Alh Garba Sanda Mani shi ne shugaban kungiyar:"Dama dai akwai hulda tsakanin kungiyar da asibitocin Jihar Katsina, kuma idan zan iya tunawa cikin azumin da ya wuce kungiyar ta biyawa wasu mutum hamsin aikin Ido irin wannan.''Wannan kungiya dai na samun karbuwa ga jama'a sakamakon aikin da take yi na taimaka wa jama'a a Jihar ta Katsina.

 

Sauti da bidiyo akan labarin