Takunkumi kan Rasha na shafar kasar Spain | Labarai | DW | 10.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takunkumi kan Rasha na shafar kasar Spain

Kasar Spain na ci gaba da fuskantar tarin matsaloli sakamakon takunkumin da kungiyar Tarayyar Turai ta kakabawa Rasha kan rikicin kasar Ukraine.

José Manuel García-Margallo

José Manuel García-Margallo

Ministan harkokin wajan kasar ta Spain ne José Manuel Garcia-Margallo da kansa ya yi wannan tsokaci yayin wani taron manema labarai a birnin Moscou tare da takwaransa na Rasha Sergueï Lavrov, inda ya ce babu wani wanda yake cin ribar wannan takunkumi da ke ci gaba da janyo musu koma bayan tattalin arziki.

Ministan harkokin wajan kasar ta Spain ya kara da cewa, kasar sa na fuskantar komabayan harkokin yawon buda ido ganin cewa Rashawa ne dama suka fi yawa cikin masu zuwa yawon buda idon, sannan ga faduwar darajar kudadan ruble na kasar ta Rasha sakamakon jerin takunkumin da aka kakaba mata, inda ya ce ya san dai nan gaba babu wani batun karin takunkumi ga Rashar, koma da yake kasar Ukraine da kanta ta tabbatar cewa dakarun 'yan awaran gabashin gasar na biyayya ga batun t