Takun saka tsakanin Jamus da kuma Amirka | Labarai | DW | 11.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takun saka tsakanin Jamus da kuma Amirka

Kasar Amirka ta kasa mayar da martani dangane da korar jami'in leken asirinta daga birnin Berlin da hukumomin tarayyar Jamus suka yi bisa sabon zargin nadar bayanai.

Gwamnatin Amirka ta ki gabatar da wata sanarwa dangane da korar babban jami'in leken asirinta da Jamus ta yi daga Berlin. Hukumomin na Jamus sun bukaci jami'in Amirkan da ya tattara nasa-yanasa ya bar kasar ne, sakamakon bankado wasu batutuwa biyu na nadar bayanai a makon da ya gabata.

Duk da cewar gwamnatin Jamus ta yi watsi da wannan batu, a siyasance ana iya cewar an sake shiga takun saka tsakanin Amirkan da Jamus, a bisa kalaman shugabar gwamnati Angela Merkel "idan hakan wani abu ne da ake ganin ya dace, ni a nawa tunanin, bata lokaci ne leken asirin wanda kuke hulda da shi, bayan akwai muhimman batutuwa da ya kamata a mayar da hankali a kansu".

Sai dai Amirkan ta ce za'a yi tattaunawar diplomasiyya kan wannan batu. A ta bakin kakakin fadar gwamnati ta White House, dangantakar Jamus da Amirka ya na da matukar muhimmanci, kasancewar suna aiki tare a fannoni daban daban. Duk da cewar a wasu lokuta ana samun sabani, Amirkan za ta ci-gaba da fuskantar wannan kalubale ta hanya madaidaiciya.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe