Takun saka tsakanin Isra′ila da Hizbullah | Labarai | DW | 28.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takun saka tsakanin Isra'ila da Hizbullah

Kasar Isra'ila ta fadawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa zata dauki duk wani mataki da ya dace wajen kare kanta ga duk wata takala daga Hizbullah.

Bayan fargabar da aka shiga ta yiwuwar fadawa cikin yanayi na yaki tsakanin bangarorin biyu.

Ron Prosor jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana a cikin wata wasika da ya turawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar Ban Ki-moon cewa ba za a lamuntaba a bari Hizbullah ta rika harin Isra'ila.

Ya ce Isra'ila ba zata bari ba a kai mata kowane irin hari akan iyakarta za kuma ta yi duk abinda da zai yiwuwu wajen ganin ta kare al'ummarta.

Wannan hari dai da ya faru a ranar Laraba ya haifar da fargaba ta sake samun yiwuwar barkewar yaki tsakanin bangarorin biyu tun bayan yakin basasar da kasashen suka shiga a shekarar 2006.

Sojan Isra'ila biyu ne da wani jami'in aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya dan kasar Spain harin makami mai linzami ya halakasu lokacin da Hizbullah ta kai farmaki kan jerin gwanon motocin sojan Isra'ila

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Pinado Abdu Waba