Takun saka tsakanin Amirka da Iran | Labarai | DW | 25.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takun saka tsakanin Amirka da Iran

Shugaba Hassan Rohani na Iran ya ce Amirka ta katse hanyoyin tattaunawa na diplomasiya, kana kuma ta yi karya a game da shelar da ta yi na neman sulhu.

Rohanin ya bayyana haka ne a jajibirin takumkumin da Amirka ta kakaba wa wasu shugabannin na Iran a ciki har Ali Khamenei jagoran addinin kasar da kuma ministan harkokin waje Mohammad Javad Zarif, na haramta musu taba kadarorinsu a kasashen waje tare da rike wasu kudaden da suka mallaka a cikin bankuna.