Takkadama kan fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai | Labarai | DW | 25.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takkadama kan fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai

Takaddama ta kunno kai inda yankin Scotland na Birtaniya zai kare matsayinsa a Tarayyar Turai bayan ficewar Birtaniya daga kungiyar.

Schottland Nicola Sturgeon in Edinburgh

Babbar ministar yankin Scotland Nicola Sturgeon

Yankin Scotland na kasar Birtaniya ya bayyana cewa zai fara tattaunawa domin kare matsayinsa karkashin kungiyar Tarayyar Turai, bayan daukacin Birtaniya ta kada kuri'ar fita daga kungiyar. Jagorar yankin Nicola Sturgeon wadda ta kira taron gaggawa na majalisar zartaswar yankin ta ce za su duba duk hanyoyin ganin kare yankin a Tarayyar Turai.

Sturgeon ta kara da cewa ganin yadda daukacin mazabun da suke yankin aka zabi ci gaba da zama cikin Tarayyar Turai haka ya nuna za a sake kiran zaben raba gardama na zama ko kuma ficewar yankin daga cikin hadaddiyar kasar Birtaniya. Sannan ta ce tabbacin zama a Tarayyar Turai ya saka 'yan yankin suka zabi ci gaba da kasancewa a Birtaniya yayin zaben raba gardama na shekara ta 2014, kuma yanzu yanayin ya sauya, saboda Birtaniya za ta fice daga Tarayyar Turai.