Takaita zirga-zirga a jihohin Borno da Yobe a Najeriya | Siyasa | DW | 03.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takaita zirga-zirga a jihohin Borno da Yobe a Najeriya

Hukumomin tsaro sun sanar da hana zirga-zirga a jihohin Borno da Yobe saboda tabbatar da tsaro a lokacin bukukuwan babbar Sallah.

Al'ummar jihar Yobe sun wayi gari da samun umurnin rufe dukkanin hanyoyi da kuma wuraren kasuwanci bayan sanarwar da kafafan yada labarai na jihar suka watsa, lamarin da mutanen jihar ke cewa ya tauye musu tagomashi da annashiwar Sallah. A jihar Borno ma hukumomin tsaron sun ayyana dokar takaita zirga-zirga saboda bukukwan Sallah kamar yadda aka yi a lokacin bukin karamar sallah da ta gabata, wanda aka ce an yi ne don tabbatar da tsaro.

Sai dai kuma a yankin arewa maso gabashin Najeriya akwai wadanda bukin Sallar ya zo musu cikin kunci da takura, inda wasu kuma Sallar ta zo musu ne suna gudun hijira, inda da dama daga cikin su suka bayyana cewa su kam ta kan su suke yi ba wai bukin Sallah ba. Kungiyoyi da dama dai sun aikewa 'yan gudun hijrar da tallafi don faranta musu rayuka, tare da kwantar musu da hankali bayan kayayyakin agaji da gwamnatin jihar Gombe ta aike musu don kara yin walwala a lokutan Sallar.

Yawancin al'ummar wannan yanki dai a iya cewa bukin babbar Sallar ta bana ta zo musu ne ciki fargaba da matsatsi, musamman saboda yadda matsalar tsaro ke kara dagulewa a wannan shiyya da ke zama mafi koma baya a ilimi da karfin tattalin arzikin.

Sauti da bidiyo akan labarin