1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddamar Saudiyya da Kanada

Yusuf Bala Nayaya
August 8, 2018

Kanada dai ta nemi Saudiyya ta gaggauta sakin 'yan fafutikar da ke tsare a kasar. Lamarin da ya bata ran mahukuntan birnin Riyadh.

https://p.dw.com/p/32nB2
Saudi Arabien Mohammed bin Salman
Hoto: Reuters/A. Levy

Tsamin harkokin diflomasiya da aka shiga tsakanin Saudiyya da Kanada ta sanya mahukuntan birnin Washington taka tsantsan wajen daukar bangare, sai dai duk da haka ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta yi ta maza inda ta nemi mahukuntan na Riyadh su bi ka'ida kan abin da ya shafi 'yan fafutikar da suke a tsare. Kanada dai ta nemi Saudiyya ta gaggauta sakin 'yan fafutikar da ke tsare a kasar.

Saudiyya dai ta kori jakadan kasar Kanada ta kuma kira nata jakadan da ya koma gida, har ila yau ta kuma katse huldar kasuwanci da mahukuntan na Ottawa, da ma tsayar da daukar nauyin daliban kasar da ke karatu a Kanada har da ma barazanar sauya masu kasar karatu, hakan kuwa na zuwa bayan da makociyar ta Amirka ta yi alawadai kan yadda Saudiyyar ke farwa 'yan fafutika.

A cewar Amirka ita na bin ka'idoji na kasa da kasa kan batun 'yanci da walwalar daidaikun mutane.