Takaddamar gwamnati da likitoci a Kenya | Labarai | DW | 16.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaddamar gwamnati da likitoci a Kenya

Kotun daukaka kara a kasar Kenya ta bayar da umurnin a saki wasu likitoci bakwai da ke zaman mambobin kungiyar likitocin kasar da ake tsare da su.

Kotu ta ba yar da umurnin sakin likitocin da aka tsare a Kenya

Kotu ta ba yar da umurnin sakin likitocin da aka tsare a Kenya

Kotun ta ce sakin liktocin ne kawai zai bayar da damar ci gaba da tattaunawar da suke da gwamnatin Shugaba Uhuru Kenyatta a kan yarjejeniyar da suka cimma a shekara ta 2013 cikin nutsuwa. A karkashin yarjejniya dai, gwamnati ta amince da ta kara yawan albashin likitocin da kaso 150 zuwa 180 tare kuma da inganta yanayin aiki. An dai cafke wadannan mambobin kungiyar likitocin kasar ta Kenya ne, bayan da suka tafi yajin aiki suna masu bukatar da lallai sai gwamnati ta cika alkawuran da ta daukar musu yayin yarjejniyar ta 2013.