Takaddama tsakanin ′yan adawa da gwamnatin Yuganda | Labarai | DW | 08.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaddama tsakanin 'yan adawa da gwamnatin Yuganda

'Yan adawa a Yuganda sun zargi gwamnatin Shugaba Yoweri Museveni da horas da mayakan sa-kai, yayin da ake shirin gudanar da zabe a badi.

'Yan adawa da masu fafutukar kare hakkin dan Adam na kasar Yuganda sun zargi gwamnatin Shugaba Yoweri Museveni da horas da mayakan sa-kai domin razana 'yan adawa yayin da ake shirin zaben kasar a shekara mai zuwa ta 2016. A makonnin da suka gabata 'yan sanda sun fara horos da dubban matasan kasar hanyoyin kare aikata laifi, da tattara bayanan sirri tsakanin jama'a.

Amma mataimakin mai-magana da yawun gwamnatin kasar ya musanta wannan zargi inda ya ce matasan sun samu horo ne cikin shirin aikin 'yan sanda tare da al'umma.

Tsakanin watannin Fabrairu da Maris na shekara mai zuwa ta 2016 za a gudanar da zaben wanda Shugaba Museveni yake sake neman wani wa'adin shekaru biyar na mulkin kasar ta Yuganda, inda zai fuskanci kalubale daga tsohon firaministansa Amama Mbabazi, kuma ana san babban wanda ya kalulanci shugaban a zaben da ya gabata Kizza Besigye zai sake takara.