Takaddama tsakanin Amirka da Falasdinu | Labarai | DW | 22.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaddama tsakanin Amirka da Falasdinu

Shugaba Mahamud Abbas na Falasdinu ya yi gargadin cewar ba za su taba amincewa ba da duk wani shirin zaman lafiya da Amirka ta tsara ba.

Mahamud Abbas shugaban Falasdinu

Mahamud Abbas shugaban Falasdinu

Mahmud Abbas wanda ya bayyana haka a birnin Paris bayan ya gana da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron. Ya ce Amirka ta zubar da kimarta a idon duniya a game da irin yadda ta yi barazana ga wasu kasashen duniya a game da kudirin MDD da ya yi watsi da kudirin Amirka a kan birnin Kudus.