1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan shirin tsaron Amirka da Ghana

Rahmatu Abubakar Mahmud LMJ
March 28, 2018

Daruruwan mutane ne suka halarci zanga-zangar lumana domin nuna kin amincewa da yarjejeniyar tsaro tsakanin Ghana da Amirka.

https://p.dw.com/p/2v9D7
Ghana Demonstration gegen Militärabkommen mit den USA
Zanga-zangar adawa da kafa sansanin sojojin Amirka a GhanaHoto: DW/I. Kaledzi

Wannan yarjejeniyar za ta bai wa dakarun sojojin kasar Amirka damar amfani da wasu sansanonin sojan kasar Ghana da rashin biyan haraji a kan duk kayan aiki da Amirkan za ta shigo da su cikin kasar tare kuma da ba ta damar kafa cibiyar sadarwa ta musamman a kyauta.

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Ghana First Patriotic Front da wasu kungiyoyin farar hula tare da wasu kungiyoyin jam'iyyun siyasa kamar NDC da APC da CPP da kungiyar daliban kasa ta NUGS ne suka halarci zanga-zangar da ta gudana a wasu manyan titunan Accra babban birnin kasar domin nuna rashin amincewarsu da yarjejeniyar.

An dai fuskanci wasu 'yan matsaloli ko da yake 'yan sanda sun taka rawa wajen dakile lamarin. Shi kuwa shugaban jam'iyyar APC Hassan Ayariya ya bayyana cewa zai shigar da kara kotu kan yarjejeniyar domin ba wai kawai yarjejeniyar ta sayar da 'yancin al'ummar kasar Ghana ba ne, kasar ma ka iya fuskantar barazanar 'yan ta'adda.

Gabanin wannan zanga- zangar dai 'yan sanda sun cafke mukaddashin magatakardan jam'iyyar NDC Kwaku Anyidoho bisa kalaman da ya yi cewar somin tabi kenan na kifar da gwamnatin shugaba Akuffo Addo. Ahalin yanzu dai ana tuhumar Anyidoho da laifin yaudara da kokarin kifar da gwamnati.