Takaddama kan shawarar karawa Jonathan wa′adin mulki | Siyasa | DW | 08.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takaddama kan shawarar karawa Jonathan wa'adin mulki

Takaddama ta kunno kai a zauren taron kasa na Najeriya, bayan da wasu wakilai suka ce a baiwa shugaban kasar karin wa’adin shekaru biyu

Bullar da wannan batu na karin wa'adin mulki ya yi a zauren taron kasa na Najeriyar ya kara nuna jan daga da masu wannan ra'ayi ke yi a cikin kasar, to sai dai ba su ji dadi ba a zauren taron domin kuwa baya ga haifar da takaddama a tsakanin wakilai bisa cewa wani kokari ne na baiwa shugaban Najeriyar karin wa'adi a mulkin kasar ta hanyar amfani da zauren taron kasar na Najeriya, abin da mafi yawan wakilai ke ganin abu ne da ba za su lamunta ba, domin baya ga rashin dacewa zai ma zubar da mutuncin taron.

Sanata Abdullahi Bala Adamu wakili a taron kasar ya ce wannan zarbabi ne kawai domin kuwa lokaci bai yi ba da za a kawo wannan batu.

"Wannan azarbabi ne kuma riga mallam masallaci za a ce dalili kuwa shi ne a lokacin da shugaban Najeriya ya kaddamar da majalisar tattaunawar nan ya nanata har sau uku cewa shi ba shi da wani buri na shi, na biyu ai ba a ma fara tattauna muhimman batutuwa a wannan taro ba, muna bayani ne a kan jawabin da shugaban Najeriya ya yi mana, don haka ta ina za a ce wai wani na ba da shawara a karawa shugaban Najeriya wa'adi a kan me? Wannan bata taso ba a bari in muka je bakin kogi ma san yadda zamu tsallake''.

Goodluck Jonathan Präsident Nigeria ARCHIV 2013

Wakilan taron sun ce karin wa'adin zai taimaka wajen aiwatar da shawarwari

Ra'ayoyi mabanbanta

Rarabuwar kawuna a tsakanin wakilan taron Najeriyar dai a kan wannan batu da karo na biyu kenan ana kokarin fito da shi a fagen siyasar Najeriyar da ke kara daukan dumi, musamman saboda kusantar zaben da Najeriyar ke fusnta ya sanya Injinya Sa'ad Abdullahi, jigo a fagen siyasar Najeriyar y ace sannu a hankali gaskiyar manufar taron ne ke bayyana a faili day a kamata a yi taka tsan-tsan.

‘'Tunda ya ke filin fadi sonka ne, zas u iya fadin komai an ce mas u duk abin da yake karkashin rana zasu iya magana a kai amma ai ba dole ba ne sai an aiwatar. In ka duba tarihi ai abinda tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya yi ke nan a irin wannan taron ya shirya, an aiwatar da abinda taron ya yi ne , domin Allah yasa wadanda suka hallarci taron suka dago abin suka ki, don haka wannan bama Magana bace amma dainata''.

Sabanin da ake samu wajen taro ba zo da mamaki ba

Duk da cewa bullar wannan batu a zauren taron kasar dai ba kasance wanda ya baiwa mutane da dama mamaki ba a Najeriyar musamman sanin cewa tun da farko an ta has ashen cewa akwai wani dalili na boye da gwamnatin ked a shin a kafa taron kasar da aka baiowa wa'adin watanni uku ya tattauna matsalolin Najeriyar in bada batun hadin kan kasa. Wa'adin da ake ganin ya yi kadan kuma was an yara ne. To sai dai ga Sanata Saidu Umar Kumo na mai bayyana cewa akwai bukatar fahimtar lamarin bisa abinda shugaban Najeriya ya bayyana tun lokacin kafa taron.

Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar

'Yan adawar Najeriya ma sun ki ra'ayin kara wa'adin mulkin

‘'Kasan in Allah ya na son kasa yakan matsa baynisa su fito da magangnu wadanda suna iya kawo tashin hankali ko matsala kafin lokacinsa ya yi, ni ban tabbatar da ma cewa shugaban Najeriya yana da bukatar wannan ba ko kuma yana da wasu a cikinmu da aka sa su su zo su yi wannan Magana. Don haka batun maganar tsawita lokaci wadanda yake son ya samu nasar wannan ba zai samu nasara ba''.

Ko da yake wakilan taron sun yi kokarin murmukse wannan batu a yanzu, amma da alama zai sake tasowa a Najeriyar domin kuwa duk da adawar day a samu a majalisar datawan kasar, masu wannan yunkuri zasu ci gaba da matsawa kamar yadda ya faru a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo. Abin jira a gani shine yadda zata kaya a tsakanin masu goyon bayan yunkurin da masu adawa das hi da ke jan nuna karfin iko a kasar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Pinado Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin