1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan matsayin Birtaniya a Turai

Kamaluddeen SaniFebruary 22, 2016

Wata sabuwar dan-barwar siyasar kasancewar Birtaniya cikin kungiyar tarayyar kasashen Turai ta barke yayin da ake shirin zaben raba gardama bisa lamarin.

https://p.dw.com/p/1Hzt6
Großbritannien Cameron und Johnson in London
Hoto: picture alliance/empics/Y. Mok

Haka biyo bayan furucin Magajin garin birnin London Boris Johnson, a inda ya futo barobaro yana nuna goyan bayan ficewar kasar daga cikin kungiyar da hakan ke kalubalantar Firiministan Birtaniya David Cameron da ya yi tinga domin ci gaba da kasancewa cikin kungiyar.

Kalaman dai na Boris Johnson da ke zama magajin garin birnin London wanda kuma yake da fada aji a harkokin siyasar Birtaniyan na zuwa ne a dai dai lokocin da Firiministan kasar David Cameron ke cigaba da matsa kaimi ga majalisun dokokin kasar wajen ganin sun ci gaba da kasancewa cikin kungiyar tarayyar Turai.

Ga abin da Boris Johnson ke cewa:

Bana tunanin akwai wani da zai amince cewar wadannan sauye-sauye da EU ko dangantakar ta Birtaniya bayan shafe tsawon shekaru 30 za a iya tsokaci, muna da dama kan yin wani abu, zan so ganin wata sabuwar dangataka kan kasuwanci.

Yayin da mgajin garin ke furta kalaman ana bangaren kuwa Firiministan Birtaniyan David cameron cewa yake:

Zan cewa Boris ne abin da nake fadawa kowa wanda zai kasance mafi sauki a gare mu, za mu bunkasa, za kuma mu inganta kan mu idan muna cikin kungiyar EU.

London Premierminister David Cameron zu den EU-Verhandlungen Downing Street in London
Hoto: Getty Images/AFP/J. Tallis

Ya kuma nuna muhimmanci kungiyoyin da kasar Birtaniya ke ciki kamar na tsaro da Majalisar Dinkin Duniya.

Ga Theresa Villers Minisata a arewacin Ireland take cewa:

Ina maraba da wannan matakin da Firiminista yake kokarin ya yi matikar kokari kuma wadannan sauye-sauyen muna maraba da su, ina ganin muna bukatar karin sauyi, ina ganin hanya daya da zamu karfafa dandantaka da Turai ita ce tattauna sabbin batutuwa a kan ciniki.

Shi ma dai Jeremy Corbyn jagoran jam'iyyar Labour mai adawa ya yi nuni da cewar:

Wannan yarjejeniya ce sabili da yakin cacar baka tsakanin wadanda suke goyan baya batun da wadanda ba sa so ga kasar da kuma Yammacin Duniya a inda David Cameron wanda yake muradin harkokin kasunci da Turai, ina ganin akwai bukatar ya kara azama sosai.

Da dama dai mutane irin su tsoffin Firiministocin Birtaniyan da suka hada da Tony Blair da John Major da ke matukar goyan bayan ganin Birtaniyan ta ci gaba da kasancewa a cikin kungiyar sun yi gargadin cewar yunkurin ficewar kasar na iya tsunduma kasar cikin wani mawuyacin hali wanda daga bisa zai kai ga silar yankewar yankin Scotland.

Brüssel EU Gipfel - David Cameron
Hoto: Reuters/D. Martinez