1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar kawancen adawa zaben Kwango

Abdourahamane Hassane
November 13, 2018

Hadaka na jam'iyyun da suka zabi Martin Fayulu dan takarar adawa a zaben shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na watan Disamba mai zuwa sun janye sakamakon matsin lamba da suka ce sun samu daga magoya bayansu.

https://p.dw.com/p/389jl
DR Kongo Martin Fayulu
Hoto: Getty Images/AFP/T. Charlier

Shugaban jam'iyyar UPDS Felix Tshisekedi da shi da na jam'iyyar UNC Vital Kamerhe sun ce sun janye daga kawancen na tafiyar tsintsiya madaurinki daya a zaben na dan takara daya tilo watau Martin Fayulu saboda bukatar da magoya banyasu suka gabatar cewar su fice. Abin da ke nufin a yanzu wanki ya koma ruwa gaba daya ga 'yan adawar na Kwango bayan taron da suka yi Geneva a makon jiya.

Magoya bayan jam'iyyu siyasa na UPDS da UNC korafin cewar dan takarar na adawa Martin Fayulu ba gogen dan siyasa ba ne da aka sanni kuma ba mamaki a hadasu a yi musu mumunar dukka a zaben na watan Disamba da ke tafe don haka suna ganin da yin muguwar rawa gwamma kin tashi..

Kusan shekaru 36 'yan adawar suka yi suna fafutukar neman hadin kai na hadin gwiwa a zaben shugaban kasar domin kayer da gwamnatin sai dai har kullum sai a kusa cimma gaci sai al'amura su dagule. Gidauniyar Kofi Annan ita ce ta kula da shirya taron yan adawar a Geneva. Kuma Bijan Farnoudi shi ne  sakataren watsa labari na gidauniyar ya kuma yi karin haske game da yadda aka yi zaben

''Dukan shugabannin 'yan adawar suka zabeshi, gidauniyar Kofi Annan ba ta shiga tsakanin ba domin neman sulhu ko sassanta 'yan adawar sune da kansu suka yi zabinsu

Ga alama dai an yanka ta tashi sannan abinda aka dade ana hasahe na rarrabuwar kawunan 'yan adawar kafin zaben ta tabbata abin da zai kara ba da dama ga dan takarar Joseph Kabila na samun mulki cikin sauki. Idan ma har an kai ga shira zaben wanda aka kwashe dogon lokaci ana dagewa.