1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama akan Sundukan makamai tsakanin Najeriya da Iran

April 30, 2013

Wata kotun a Najeriya ta ce ta kammala shirye shiryen yanke hukunci bisa zargin Iran da safarar makamai ta Najeriya ta haramtacciyar hanya.

https://p.dw.com/p/18PhE
TO GO WITH AFP STORY BY JOEL OLATUNDE AGOI (FILES) A file photo taken on April 12, 2005 shows the Apapa Terminal parked full with containers in the main Nigerian seaport in Lagos. Since January 2009, the Nigerian Ports Authority (NPA) has been battling to clear Lagos port of congestion, which has been building up since October 2008 and which has led to several thousand containers being abandoned there. Every month, an average of 70 vessels -- container ships and oil tankers -- arrive in the Lagos port in addition to thousands of overtime containers abandoned by importers and customs agents because of complaints over high charges. AFP PHOTO / PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: AFP/Getty Images

Wani alkalin kotun tarayya da ke birnin Legas a Najeriya, ya jinkirta yanke hukunci game da shari'ar da ta shafi wani jami'in rundunar juyin juya halin kasar Iran da ake zargi da hannu wajen safarar makamai ba bisa ka'ida ba ta Najeriya. Azim Aghajani - dan asalin kasar ta Iran, da kuma Ali Abbas Jega- dan Najeriyar da ake zarginsa da hadin baki da shi wajen safarar makamai ta tashar jiragen ruwan Najeriya dai, sun bayyana a gaban kotun - a wannan Talatar, yayin da alkalin kotun tarayya Okechukwu Okeke ya bayyana cewar saboda sarkakiyar da ke tattare da shari'ar ta su, yana bukatar karin lokaci domin yanke hukunci a ranar 13 ga watan Mayun nan da ke tafe.

Shi kuwa Lauyan da ke kare wadanda ake zargin, Chris Uche, cewa yayi yana da kyakkyawar fatan cewar hukuncin kotun zai wanke Azim Aghajani, dan Iran din daga zargin da ake yi masa.

Dama dai a shekara ta 2010 ne hukumomi a Najeriya suka tsare wasu manyan Sundukai ko kuma Kontenoni 13 dauke da makamai a tashar jiragen ruwn Apapa da ke Legas a Najeriya, inda suka yi zargin cewar dan kasar ta Iran na kokarin safarar su ne zuwa kasar Gambia, kuma tun cikin watan Fabrairun 2011 ne ake yiwa dan Iran din shari'a tare da wani dan Najeriyar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou