1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama a tsakanin matakan gwamnatoci uku na Najeriya

September 27, 2013

Rashin kudaden gudanar da mulki na neman jefa hukumomin Najeriya cikin tsaka mai wuya.

https://p.dw.com/p/19piw
Nigerian Finance Minister Ngozi Okonjo-Iweala speaks at a press conference of African finance ministers at the 2013 World Bank/IMF Spring meetings in Washington on April 20, 2013. AFP PHOTO/Nicholas KAMM (Photo credit should read NICHOLAS KAMM/AFP/Getty Images)
Hoto: NICHOLAS KAMM/AFP/Getty Images

A wani abin da ke zaman alamun kara shiga cikin rudani a matakan gwamnatocin tarayyar Najeriya, ana ci gaba da takaddama a tsakanin jihohin da ke korafin rage musu kaso na wata wata da kuma gwamantin kasar da ta ce har yanzu fa ba matsala ga batun kudin shigar kasar ta Najeriya.

Babu dai zato ba kuma tsammani dai babbar ministar tattalin arzikin kasar ta Najeriya ta fito ta ce tana shirin ta tsaya a cikin harkokin kudin tarayyar Najeriya daga karshen wannan wata da muke ciki.

Ngozi Okonjo Iweala dai ta ce batu na biyan albashi dama ragowar yau da kullum na gwamantin na shirin shiga hali na rashin tabbas sakamakon karancin kudin da kasar ta Najeriya ke fuskanta. Matakin kuma da sannu a hankali ke kara bayyana a tsakanin matakai daban daban na kasar da ke korafin ragowar kudin shiga aljihunsu.

Jan. 9, 2012. Labor unions began a paralyzing national strike Monday in oil-rich Nigeria, angered by soaring fuel prices and decades of engrained government corruption in Africa's most populous nation. (Foto:Sunday Alamba/AP/dapd)
Jerin gwanon kungiyar kwadago a NajeriyaHoto: dapd

An tashi baram baram a taron rabon arzikin kasa

Sau biyu cikin tsawon mako biyu ne dai kwamishinonin kudin jihohin kasar na taro a Abuja, sau biyun kuma taron na watse wa a baran baran, sakamakon karancin kudin da ya bata ran jihohin da wasunsu ma suka nemi ministar kudin kasar da ta sauka, sakamakon gazawar tafi da harkokin kudin kasar kamar yadda ya dace.

Bayan nan dai suma 'ya'yan sabon bangare na PDP dai sun tada kara ga abin da suka kira daukar kasar ta Najeriya zuwa rushewa a bangaren shugaban kasar da a cewarsu ya rude ga batun na tattalin arziki.

Har ya zuwa yanzu dai a cewar mabiya na sabuwar PDP, gwamnatocin jihohin kasar na bin tarayya basuka na kasonsu na watannin Juni da Juli dama Augustan jiya, a wani abin da ke zaman alamu na rushewar tattalin arzikin kasar, da kuma a cewar Mallam Usman Balkore da ke zaman wani masani na tattalin arziki ke da ruwa da tsaki da halin bera na mai da ma kudinsa da yanzu haka ke zaman ado tsakanin yan bokon kasar ta Najeriya.

Treffen nigerianischer Gouverneure. Foto: DW-Korrespondent Ubale Musa, 26.6.2013 in Abuja
Taron gwamnonin NajeriyaHoto: DW

Wasu jihohin Najeriya na fuskantar matsalar gaza biyan bukatun al'umma

Ya zuwa yanzu dai akalla jihohi uku ne suka fito suka yi korafin abin da suka kira kokarin tsayawar lamuransu, a wani abin da ke zaman alamu na kara shiga rudanin dama kila sabon rikici a tsakanin bangarorin dake dogaro da kudin shigar tarayya domin rayuwarsu ta yau da kullum.

To, sai dai kuma a cewar Dakta Yarima Lawal Ngama da ke zaman karamin ministan kudin kasar, korafe korafen dama matakan kaurace wa tarukan rabon kudin sunfi kama da siyasa maimakon kokari na gyaran tattalin arzikin tarayyar Najeriya.

Abin jira a gani dai na zaman mafita a cikin sabon rikicin da ke kara ta'azzara, a dai dai lokacin da tarayyar Najeriya ke tsakanin warware rikici na siyasa da kuma cika alkawarin 'yan kasar, na sauya rayuwa a cikin kankanen lokaci.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh