1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina ta mayarwa Amurka martani

Ramatu Garba Baba
July 15, 2020

Fadar Beijing ta mayar da martani kan matakin da Shugaba Donald Trump ya dauka na janye yarjejeniyar kasuwancin da aza ma manyan jami'an gwamnatinta takunkumi, bisa zargin Chainan da kokarin son mamaye yankin Hong Kong.

https://p.dw.com/p/3fLY6
Symbolbild USA China Beziehungen
Hoto: imago images/B. Trotzki

Fadar Beijing ta sha alwashin daukar matakai daidai da wadanda Amurka ta dauka na sanya mata takunkumi, martanin Chainan ya biyo bayan matakin da Amurkan ta dauka na bai wa Hong Kong damar kasancewa da zama yankin mai cin gashin kai daidai da na Chainan. A jiya Talata ne Shugaba Donald Trump ya sanya hannu kan kudurin dokar da ta ba shi damar aiwatar da wannan hukuncin.

Sabuwar takaddamar ta biyo bayan dokar tsaron da China ta kakaba a yankin Hong Kong, wacce ta tanadi hukuncin daurin rai da rai ga wadanda aka kama da laifi, bayan majalisar dokokin China ta kada kuri'ar amincewa da ita, tare da bai wa kotun China damar zartar da hukunci ga wadanda aka kama da aikata munanan laifuka da suka saba dokar a yankin Hong Kong.