Takaddama a kan ingancin tsagaita wuta a arewacin Najeriya | Siyasa | DW | 12.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takaddama a kan ingancin tsagaita wuta a arewacin Najeriya

Cece-kuce na ci gaba da mamaye shirin tsagaita wutar da gwamnatin Najeriya ta sanar a tsakaninta da 'ya'yan kungiyar Boko haram.

A baya dai an musu kallo na masu maida rikici hanyar tara abun duniya, har ma an zargesu da taka rawa wajen ruruwar rikicin tsaron da ya mamaye sashen arewacin tarayyar Najeriya, ga rundunar tsaron kasar da ta share tsawon lokaci tana adawa da duk wani kokarin sulhu da 'ya'yan kungiyar Boko haram,

rundunar kuma da daga dukkan alamu har yanzu ke adawa da shirin tsagaita wutar da kwamitin gwamnatin kasar kan afuwar ya sanar a cikin makon da muke ciki.

Sojojin da yanzu haka ke kan gaba ga kokarin aiwatar da tabbacin da ta kai ga farautar 'yan kungiyar ya zuwa birni da kauyukan rikicin dai, tace har yanzu ba ta samu bayanin afuwar ba duk da ganawar da 'yan kwaimitin suka kai ga yi da shugabannin hafsoshin tsaron kasar a ranar Laraba (10.07.13).

An dai ruwaito kakakin sojan kasar ta Najeriya, Janar Chir Olukolade na cewa, babu hannunsu a cikin shirin tsagaita wutar sannan kuma babu masaniyarsu da halin da kwamitin da 'ya'yansa suka kunshi wakilan sojan ke ciki har ya zuwa yanzu.

Rawar rundunar soji a rikicin Boko Haram

Ana dai kallon sabon ikirarin a matsayin wani kokari na maida hannun agogo can ya zuwa baya, ga tarayyar Najeriyar da ke ikirari na kaiwa ga gano baki ga zaren.

A farkon wannan mako ne dai ne wakili, kuma mataimakin shugaba ga kungiyar ta Boko haram, Imam Mohammed Marwan ya ce sun yanke shawarar tsagaita wutar, tare da yawu da amincewar shugaba ga kungiyar Abubakar Shekau.

Magana da yawu na imam Shekau ko kuma kokari na gaban kai dai, ko bayan sojan kasar ta Najeriya dai ita ma kungiyar Kiristocin kasar ta C A N ta ce a kai kasuwa game da shirin tsagaita wutar da ya ce ya makaro kuma bashi da tasiri.

Autor: Ubale Musa (Korr DW).in Abuja, Nigeria Below are the pictures of the arrival of the security meeting PIC FROM LEFT: CHIEF OF DEFENCE STAFF, ADMIRAL OLA IBRAHIM; CHIEF OF ARMY STAFF, LT.-GEN AZUBUIKE IHEJIRIKA AND CHIEF OF DEFENCE INTELLIGENCE, MAJOR-GEN. SANI AUDU ARRIVING FOR A MEETING AT THE PRESIDENTIAL VILLA ABUJA ON THURSDAY (4/3/13)

Shugabanin rundunonin tsaro a Najeriya

Ra'ayin masana a kan ingancin kokarin sulhu

To sai dai kuma ana kallon adawar sojan a matsayin matsala mafi girma da ka iya fuskantar kwamitin da ya share kusan tsawon watanninsa uku yana kai kawo da nufin shawo kan 'yan kungiyar da a baya suka yi nasarar tada hankali a daukacin kasar.

To sai dai kuma a cewar mallam Faruk B. B. Faruk da ke zaman masanin harkoki na siyasa a jami'ar birnin tarraya na Abuja, a al'adance soja a ko'ina a duniya ba su cika son mika wuya da karatun sulhu da 'yan sunkurun da suke yaka ba.

Abun jira a gani dai, na zaman mafitar 'yan kwamitin da yanzu haka ta tabbata ke da sababbin abokai na hamayya a cikin rundunan tsaron da ke kokarin nuna karfi na hatsi na zaman mafita ta kadai ga rikicin da ke cikin shekararsa ta hudu.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin