Taimakon wadanda rikicn Boko Haram ya shafa | Himma dai Matasa | DW | 25.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Taimakon wadanda rikicn Boko Haram ya shafa

A Jihar Tabara da ke Najeriya an samu wani dan kasuwa da yake horas da mata wadanda rikicin Boko Haram ya raba da mazajensu.

Adamu Muhammad Shellen, wani mutum da ya jajirce don taimakon mata da suka rasa mazajensu aakamakon rikicin Boko Haram da fadace -fadacen kabilanci da aka samu a Jihar Taraba da ke Najeriya. Shi wannan dan kasuwa yana horas da daruruwan mata sana'o'in, kamar  yin worworo da abin kunne da sarkar wuya da kuma takalma. Haka kuma akwai mata sama da 50 da suke amfana da koyon sanar a jahar.