Taimakon matasa likitoci | Himma dai Matasa | DW | 30.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Taimakon matasa likitoci

Likitotin 'yan Jihar Katsina da ke Najeriya sun kirkiro hanyoyin taimakon marasa lafiya wadanda ba su da galihu da ke zaune a jihar.

Matasan likitoci yan asalin Jihar Katsina da ke aiki jihohi daban-daban sun gudanar da wani babban taro a shekarar da ta gabata da nufin lalubo hanyoyin da za su ba da gudummuwa ga al'ummar jihar marasa lafiya, inda suka cimma matsayar bin kowace karamar hukuma su tara marasa lafia suyi masu aiki akan ciwon da suke fama dashi kyauta.

Yanzu haka dai sun fara da karamar hukumar Kankara inda sukaiwa mutane 250 aiki akan laruru iri daban daban kuma kyauta a babban asibitin karamar hukumar ta Kankara,

Dr Muhammad Umar shi ne ya jagoranci wannan aiki yace sai da suka tintibi duk bangarorin da suka kamata dan samun nasarar aikin. Ba da gudummuwa ga al'ummar ka abu ne me mahimmanci dan masu iya magana kan ce kowa yabar gida gida ya barshi Yusuf Ibrahim Jargaba DW hausa daga katsina a Nigeria.