Taimakon marasa karfi | Himma dai Matasa | DW | 03.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Taimakon marasa karfi

Wani matashi a birnin Abuja na Najeriya mai suna Ayodele Edwart ya sami lambar yabo daga kasar Kanada sakamakon fafutukar da yake wajen taimakon marasa karfi a cikin alumma  ta hanyar ganawa dasu domin share musu hawaye.

Matashin wanda ya shafe shekaru a Amirka ya ce ya zama wajibi a karan kansa ya fara fafutukar ganin ya taimaki marasa galihu ta hanyar tattara bayanan da yake samu sakamakon cibiyar da ya samar mai suna (RIVAC) wacce yake karbar korafe-korafen al'umma bayan da ya komo Najeriya a inda daga bisani yake isar da su ga wadanda alhakin kula da su ya shafa.

Kazalika Mr Ayodele Edwart ya shaida cewar babban dalilin daya zaburar dashi wannan fafutukar da yake wajen tallafawa jama'a a fannoni da dama kama daga samar da burtsatse giggina gadoji gami da tallafawa yaran da iyayen su ba su da galihu da kayyayakin karatu.

Bugu da kari Ayodele Edwart ya ce babban kalubalen shi ne kudaden da suke gudanar da ayyukan na kyautata rayuwar jama'a.

Yanzu haka dai Ayodele Edwart ya ce babban burin sa shi ne fargar da mutane tare da yin iyakacin kokarinsa wajen share musu hawaye gwargwadon karfinsa.