1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimakon jama'a da son juna lokacin Kirsimeti

Umaru AliyuDecember 24, 2012

Ranar 24 ga watan Disamba, lokaci ne mai muhimmanci ga mabiya addinin Kirista, saboda kasancewarsa lokacin fara bukukuwan Kirsimeti.

https://p.dw.com/p/178Tp
Hoto: Florian Mebes

A nan Jamus, akan kwatanta ranar ta yau a matsayin "Heiligabend" wato dare mai tsarki, kuma lokaci na haduwar iyali da yiwa juna barka da sake kewayowar wnnan rana. Jamusawa da yawa sukan yi amfani da ranar domin shirya abinci ga masu bukata, musamman wadanda ke fama da zaman kadaitaka da marasa galihu ko wadanda basu da wuraren zama.

Ga Peter Kühweidler, yau, ranar da ake kwatanta ta da suna dare mai tsarki, takan fara ne gareshi tun misali karfe hudu na asuba a dakin dahuwar abinci, inda yake da alhakin shirya abinci iri dabam dabam ga mutane akalla 120. Wadannan mutane kuwa ba baki ne da shi kansa ya gaiyace su ba, kamar danginsa ko abokansa ko wasu yan uwa na nesa da na kusa. Peter Kühweidler zai tanadi abincin ne ga mutane marasa galihu, masu fama da talauci, ko marasa wurin zama a wani dan karamin gari mai suna Wesseling kusa da Coogne. Idan kukun ya kammala dahuwarsa, ya kwashi abinda ya dafa zuwa ga wadanda suka taru, to shi gareshi, a wannan lokaci ne aka fara bikin Kirsimeti.

Yace abin farin ciki ne ka ga yadda wadannan mutane suke tururuwa zuwa katon dakin cin abinci da na tanada. Matata ko wace shekara abu guda ta kanji, wato yadda bakin suke farin cikin baiyana abubuwan da suka taras a dakin, to amma abin farin ciki ne mutum ya ga yadda idanunsu suka yi haske, suna baiyana godiya da gamsuwa da farin cikinsu.

Peter Kühweidler yace masu zuwa su ci abincin ba suke nan aka saba gani a ko wace shekara ba. Akan sami sabbi, misali yan gudun hijira da musulmi da kiristoci dakan taru a wnanan dare mai tsarki. Wannan abinci da yakan tanada a ko wace shekara a irin wannan rana, yakan zama kamar dai godiya ne ga irin taimakon da shi kansa ya samu a matsayinsa na maraya lokacin da yake zaune a Austria. Kühweidler ba shi kadai ne yakan tanadi abinci ga marasa galihu, ko tsoffi dake zaune su kadai ko yan gudun hijira ba. Sanannen mawakin nan na Jamus, Frank Zander shima yakan shiryawa mabukatan lokaci na cin abinci a duk ranar 24 ga watan Disamba, inda a bana, wadanda zasu dauki nauyin raba abincin ga mutanen da aka gaiyata 2800 sun hada har da shugaban jam'iyar Greens, Cem Özdemir da dan wasan boxing Graciano Rocchigiani.

Kulturkalender Dezember Adventskalender Weihnachten
24 ga watan Disamba, ranar fara bikin KirsimetiHoto: Fotolia/Stefanie Maertz

A irin wannan rana, marasa galihu ko wadanda basu da wurin zuwa, musamman sukan kasance a wani hali na kaka-ni-kayi. To sai dai Marita Hoff tace ba irin wadannan mutane kadai zaman kadaitaka takan kawo damuwa garesu ba. Marita Hoff takan shirya bikin Kirsimeti a ko wace shekara inda duk mai bukata yake iya zuwa domin haduwa da sauran jama'a a wani dan karamin gari mai suna Hof, kusa da birnin Bremen a arewacin Jamus.

Tace watarana na lura da cewar wata daliba matashiya tana daga cikin wadanda suka zo wurin wannan biki. Da na tambayeta abin da ya sanya bata je wurin iyayenta domin su yi bikin Kirsimeti tare ba, sai ta shaida mani cewar tayi fada ne da iyayenta, bata son zuwa wurinsu, amma kuma bata son zama ita kadai a dakinta a gidan dalibai.

Deutschland Adventskalender Weihnachtsmann in Himmelpfort
Father Christmas mai rabawa yara kyaututtukaHoto: picture-alliance/dpa

Hoff tace a irin wannan rrana, ko a wnanan dare mai tsarki, babu wani mutum da ya cancanci zaman kadaitaka, saboda wannan lokaci ne na nuna zumunci da kaunar juna da son jama'a.

Mawallafi: Regina Menning/Umaru Aliyu
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani