1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Ana taimakon lokacin Azumi

April 5, 2022

A Jihar Kebbi da ke shiyar arewa maso yammacin Najeriya kungiyoyi na ta fadi tashin taimakon marasa galihu da masu dan karfi musamman don ganin sun gudanar da Azumin Ramadana cikin kwanciyar hankali da kuma walwala.

https://p.dw.com/p/49UXX
BdT Pakistan Essen in Ramadan
Hoto: AP

Ana raba abincin kenan, kuma kadan daga cikin tarin wasu mata marassa lafiya da suka amfana a garin Argungu na jihar Kebbi, sun bayyana irin jin dadi tare da farin ciki ga kungiyar "Patients and Destitute Welfare Organizations" wato PADWO bayan da kungiyar ta kaddamar rabon kayan abinci ga marasa lafiya a asibitocin garin, da kuma mutane marasa galihu a cikin al'umma.

Kayan buda baki iri-iri na daga cikin abubuwan da kungiyar ta ke tallafawa masu dan karfi majinyata da sauran ‘yan Rabbana ka wadatamu, kuma tuni malammai da sauran masu fafutukar ganin a taimakawa marassa galihu ke ta ankarar da jama'a muhimmacin taimakawa mabukata musamman a wannan wata na Ramadan.

Yayin da ake ta dan-dana ukubar tashin farashin kayan masarufi a Najeriyra irin wannan taimako da kungiyoyi irin PADWO ke yi ga al'umma ko shakka ba bu za su rage wahalhalu su kuma taimaka musamman ga masu karamin karfi.