1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taimako na sojoji ga Afirka ta Tsakiya

November 26, 2013

Yanayin da ake ciki a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na kara sukurkucewa a bangaren tsaro. saboda haka Faransa za ta kara dakarunta a wannan kasa.

https://p.dw.com/p/1AP5X
Hoto: Reuters

Kasar ta Faransa wadda yanzu haka take da kimanin dakaru 400 a kasar ta Jamhuiriyar Afirka ta Tsakiya, wadanda mafi yawa da kula da harkokin sufuri na filin saukan jiragen saman Bangui babban birnin kasar, ta damu da tabarbarewar lamura a cikin kasar. Tuni Faransa ta ce a shirye take wajen aikewa da karin dakaru 800.Kasashen duniya na bayyana fargabansu a kan ta'adin da ake tafkawa na aikata kisan gilla da fyade. Bruno-Yacinthe Gbiegba na wata kungiyar kare hakkin dan Adam da ke Bangui babban birnin kasar ga bayanin da ya yi bisa halin da ake ciki:

"Akwai 'yan tawaye da masu tsananin ra'ayi wadanda suke aiwatar da kisan gilla. Kuma wannan shi ne abin tsoro. Ana kashe mutane saboda dalilan kabilanci da addini, wannan abu ne da ya dace a dakile"

A cewar wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya kimanin kashi daya cikin hudu na al'ummar kasar milyan hudu da rabi na cikin hali na bukatar agajin abinci da magunguna. Mafi yawan mutanen sun tsere daga hare-haren tsaffin 'yan tawaye na kungiyar Seleka ko kuma magoya bayan tsohon Shugaba Francois Bozize, wanda aka kifar da gwamnatinsa cikin watan Maris. Yanzu tashe-tashen hunkula ana samu tsakanin Kiristoci masu rinjaye da kuma Musulmai marasa rinjaye.

Zentralafrikanische Republik November 2013
Hoto: Pacome Pabandji/AFP/Getty Images

A cikin watan Maris na wannan shekara ta 2013, 'yan tawaye suka kifar gwamnatin Bozize, inda Michel Djotodia ya karbi madafun iko. Firaministan kasar Nicolas Tsangaye ya ce kamata ya yi a hanzarta tura dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, tare da tabbatar da aiki da babi na bakwai na kundin Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya baiwa dakarun ikon amfani da karfi. Bruno-Yacinthe Gbiegba na wata kungiyar kare hakkin dan Adam, yana da irin wannan tunani:

"Wannan halin da ake ciki babu mai bukatar ya ci gaba, shi ya sa muke goyon bayan kawo sojojin Faransa, domin suna sane da abin da ke faruwa, kuma za su iya magancewa. Kuma da sauri ya dace sojojin su iso farawa da Faransa.

Yanzu haka ana shirin gudanar da taro cikin tsakiyar watan Disamba, domin karfafa aikin dakarun kiyaye zaman lafiya na Afirka, kuma bayan daukan kudirin taron za a kara yawan sojojin Faransa da ke kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. A wani zaman da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi, Faransa ta ce za ta ajiye wani daftarin kudiri a gaban majalisar na sake dawo da doka da oda a kasar da ta fada cikin rudani da rashin tabbas. Mataimakin Sakatare Janar na majalisar Jan Eliasson ya yi gargadi kan rudanin da kasar za ta shi, sannan ya nemi Kwamitin Sulhu ya karfafa dakarun kiyaye zaman lafiya na Afirka 3000.

Zentralafrikanische Republik Vereidigung Michel Djotodia
Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Michel DjotodiaHoto: STR/AFP/Getty Images

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohamadou Awal Balarabe