Tahirin marigayi Ado Gwadabe | Amsoshin takardunku | DW | 13.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Tahirin marigayi Ado Gwadabe

Marigayi Ado Gwadabe ya je Rasha alokacin ana tsoron ra'ayin gurguzu kuma shi ne tsohon shugaban Sashen Hausa na DW.

50 Jahre Haussa Redaktion

Daga hagu zuwa dama marigayi Ado Gwadabe da Yahaya Musa da Ibrahim Maccido da Muhammad Sani Dauda cikin shirin Ra'ayin Malamai

Marigayi Ado Gwadabe tsohon shugaban Sashen Hausa na DW an haife shi a shekarar 1939 a birnin Kano da ke Najeriya, kuma ya bar duniya ranar 21 ga watan Yuni na 2015, yana da shekaru 76 a duniya.

Kuma ya yi karatu a birnin Kano kafin zarcewa zuwa birnin Moscow na kasar Rasha, inda ya kara karatu, daga bisani ya fara aiki da tashar DW. Kafin ya tafiya kasashen ketere marigayi ya yi aikin koyarwa a wasu kananan makarantu da ke birnin Kano.

Marigayin ya fara aiki da DW a farkon shekatru 1970, sannan ya zama shugaban Sashen Hausa a shekarar 1993 inda ya yi shugabancin zuwa 2004.

Ya bar mata da yara hudu.