1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tagomashi a shirin kasuwancin Turai da Kanada (CETA)

October 28, 2016

Tattaunawar kawancen cinikayya tsakanin Kanada da Kungiyar Tarayyar Turai (CETA) za ta yi sanadi na bude kasuwa ga mutane miliyan 500 a Turai.

https://p.dw.com/p/2RqH8
CETA Kanada EU Handelsabkommen
Hoto: picture-alliance/dpa/K.Ohlenschläger

A yanzu dai kungiyar tarayyar Turai ta shirya cimma gagarumar yarjejeniya mai dumbun fata da kuma buri da aka dade ana jira ta kawancen cinikayya tsakanin tarayyar Turai da kasar Kanada, bayan tsawon mako guda bangarorin biyu na tafka zazzafar muhawara.

Tsawon kwanaki yankin Wallonia na kasar Beljiyam da ke amfani da harshen faransanci ya hana ruwa  wajen cimma yarjejeniyar wadda ke nufin dage shingen cinikayya tare da saukaka shige da ficen kayayyaki tsakanin kanada da tarayyar Turai.

A karshe dai a jiya mashawarta na kasar ta Belgium tare da majalisun dokokin yankin suka cimma masalahar amincewa da yarjejeniyar kamar yadda Firaministan kasar Charles Michel ya shaidawa 'yan jarida.

" Ina farin cikin sanar da cewa yanzun nan kwamitin da ke tattaunawa ya cimma masalaha kan daftarin yarjejeniyar wadda ta fayyace bukatun Belgium wadda kuma za'a mika ta ga kungiyar tarayyar turai da kuma shugaban majalisar Turai."

Shi ma dai a nasa tsokacin gwamnan yankin Wallonia mai amfani da harshen Faransanci Paul Magnette ya baiyana jinkirin da aka samu a tattaunawar da cewa alheri ne:

Deutschland SPD-Parteikonvent in Wolfsburg
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Stratenschulte

"Idan an sami jinkiri kadan, hakan a gani na alheri ne idan aka yi la'akari da nasarar da muka cimma, wanda ke da muhimmanci ba wai ga yankin Wallonia kadai ba har ma ga Tarayyar Turai baki daya."

Amincewar ta Kanada dai ta ceto yarjejeniyar daga durkushewa baki daya. Sai dai kuma duk da wannan matsayi a waje guda ministar cinikayya ta kasar Kanada Chrystia Freeland ta ce har yanzu akwai sauran aiki a gaba. Abin tambayar ita ce me wannan yarjejeniya ke nufi ga dangantakar cinikayya da sauran kasashe kamar Amirka kuma wane tasiri zai yi? Sigmar Gabriel ministan tattalin arzkikin Jamus ya yi bayani da cewa:

"Yadda duniya ke cigaba haka ma harkar cinikayya ke ci gaba. Batun shi ne yaya muke so mu tsara dokokin cinikayya da wasu manyan kasashe kamar China da Amirka.? Ina gani abu ne mai kyau da muka fara da Kanada domin babu wata kasa da ta fi kusanci da tarayyar turai kamar Kanada".

Babban fata a cewar shugaban majalisar tarayyar Turai Martin Schultz shi ne cewa yarjejeniyar cinikayyar ta CETA za ta bude kasuwa ga mutane miliyan 500 a Turai kasancewar nahiyar daya daga cikin kasuwanni mafi girma a duniya.