Tabbatar da daurin shekaru 50 a kan Taylor | Labarai | DW | 26.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tabbatar da daurin shekaru 50 a kan Taylor

Alkalin kotun daukaka kara da ke birnin Hague ya tabbatar da hukuncin farko da aka yanke wa tsohon shugaban kasar ta Liberia Charles Taylor a watan Mayun 2012.

Kotu ta musamman dake da zama a birnin Hague, wadda ke da goyon bayan Majalisar Dunkin Duniya ta tabbatar da daurin shekaru 50 a kan tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor. A bara ne dai aka yanke wa Taylor mai shekaru 65 da haihuwa, hukuncin zaman gidan kurkuku na shekaru 50, saboda samunshi da taimaka wa kungiyar 'yan tawaye a lokacin yakin basasar kasar Saliyo dake makwabtaka da Liberia.

A yayin da ya ke watsi da karar da Mr Taylor ya shigar gabansa, Alkalin kotun ya ce an yi adalci a hukuncin farko da aka yanke masa. Lauyan tsohon shugaban na Liberia dai, ya nemi kotun da ta soke hukuncin tare da wanke shi, saboda kuskuren da ya ce an samu a lokacin shari'arsa a baya. Sai dai kotu ta yi watsi da bukatun masu shigar da kara na kara wa'adin zaman kurkun daga shekaru 50 zuwa 80.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh