Tabarbarewar sha′anin tsaro a Najeriya sakamakon sace-sacen jama′a | Siyasa | DW | 26.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tabarbarewar sha'anin tsaro a Najeriya sakamakon sace-sacen jama'a

Gwamnatin jihar Delta a Najeriya ta bayyana gano wasu boyayyun sansanonin horar da ma su halayyar satar mutane da ke karbar kudaden fansa.

Gwamnan jIhar Delta, Cif Emmanuel Uduaga, shine ya tabbatarwa da wasu jama'a a jIhar cewar tare da hadin gwiwar jami'an tsaro ne gwamnati ta bankado wasu gurare da ake baiwa dukkannin masu tafka ta'asar makamar sanin dabarun iya satar mutane don garkuwa da su, da nufin karbar kudaden diyya, da ke bobboye a jahar ta Delta.

Gwamnan ya kuma ce a halin yanzu gwamnati na baiwa jami'an tsaron jihar dukkanin goyon baya da tallafi a aikin ganin an dakile matsalar wadannan bata-gari 'yan satar mutane don karbar kudin fansa, da suka dade suna haifar da nakasu a harkokin yau da kullum a jihar.

Image made available on 19 September of militants from the Movement for the Emancipation of the Niger Delta (MEND) as they patrol the volatile oil rich creeks of the Niger delta in Nigeria 18 September 2008. The Movement for the Emancipation of the Niger Delta claimed in a statement on 19 September 2008 it has attacked a pipeline operated by Shell. MEND declared 'war' on Nigeria's oil industry a week ago. EPA/GEORGE ESIRI +++(c) dpa - Bildfunk+++

Martani game da matsalar satar jama'a

Ko da yake dai matsalar ba a jihar Delta bane kawai, daukacin jihohin Niger Delta da ma yankin kudu maso gabashin Najeriya, satar jama'a don samun kudin fansa, al'amari ne da ke dada kazanta, kamar ma dai yadda wani Mallam Mustafa dan kabilar Igbo ke cewa:

"Wannan al'amari dai na cewar akwai wasu gurare da ake bada horon sanin makama a fannin satar mutane don garkuwa da su, za a iya cewar sabon batu ne, koda yake wasu ma sun lura da al'amura na ganin cewar, harka ta satar mutane don garkuwa da su ta rigaya ta zama wata ma'aikata mai zaman kanta a Najeriya da ke samar da ayyukan yi a kasar, bisa la'akari da kamar yadda wasu ke ganin cewar ayyukan yi sun yi karanci a kasar.

Maganar ma dai da ake yi, matsalar ta satar mutane don garkuwa da su, matsala ce da ta riga tayi girman tasiri a sassa daban daban na Najeriya, yanayin kuma da ke dada bata sunan kasar a idon duniya, tare da kuma haifar da sake tunani ga masu jimirin saka jari a kasar.

Yunkurin dakile matsalar satar jama'a

Mallam Muhammadu Musa Katsina, kwamishinan 'yan sanda ne a jahar Imo da ke kudancin kasar, kuma ko da yake bai dade da zuwa jihar ta Imo ba, ya bayyana min kalubalen da zai tunkara a aikinsa da ya hada da kokarin dakile 'yan satar mutane don garkuwa da su, tare kuma da karin bayani kan abinda suke bukata daga jama'a don cimma nasarar aikinsu na 'yan sanda a tsaron jama'a da dukiyoyinsu.

Wani abin takaici dai da mutane da yawa ke furtawa, shine na yadda alkaluma suka nunar da yadda ake samun dalibai na gaba da sakandare da na jami'oi a Najeriyar cikin muggan ayyuka da suka hada da satar mutane dan garkuwa da su da ma fashi da makami.

Ko da yake dai wasu jihohi a Najeriyar sun samar da dokar hukuncin kisa ga yan garkuwa da mutane din, wasu jihohi da dama dai na hangen son yin haka.

Mawallafi : Muhammad Bello
Edita : Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin