Tabarbarewar al′amura a Ukraine | Labarai | DW | 12.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tabarbarewar al'amura a Ukraine

Kungiyoyin kasa da kasa sun nuna fargabar yiwuwar kara tabarbarewar al'amura a gabshin Ukraine da 'yan aware masu goyon bayan Rasha ke jagoranta.

Kungiyar Tsaro da Hadin Kan Turai da ke sanya idanu a rikicin na Ukraine OSCE ta ce akwai alamu da ke nuni da cewa yanayin da ake ciki a yankin gabashin Ukraine da ke fama da yaki zai rincabe. Wanna dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da jakadan kasar Ukraine a Majalisar Dinkin Duniya Yuriy Sergeyev ke yin korafin cewa ya kamata majalisar ta sani Rasha na kokarin mamaye Ukraine, yana mai cewa alamu na baya-bayan nan sun tabbatar da kudirin na Rasha. Dama tuni kasashen yamma da ke goyon bayan gwamnatin Kiev din ke zargin mahukuntan na Moscow da iza wutar rikicin, batun da Moscow ke ci gaba da musantawa, ta na mai cewa kare muradunta da ke gabashin kasar ne kawai ta ke yi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu