Tababa kan asalin Ali Bango shugaban kasar Gabon | Labarai | DW | 25.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tababa kan asalin Ali Bango shugaban kasar Gabon

'Yan adawar kasar ta Gabon na zargin Shugaba Ali Bango da kasancewa dan asalin kabilar Igbo ta Najeriya da Omar Bango da dauko riko a lokacin yakin Biafra.

A kasar Gabon wata sabuwar takaddama ce ta sake kunno kai tsakanin bangaran gwamnati da kuma 'yan adawa dangane da batun asalin Shugaban Kasar Ali Bango Ondimba bayan da wata babbar cibiyar kula da harakokin takardun haihuwar ta kasar Faransa ta fito da wata takardar haihuwa da ke neman nunar da tabbacin cewa Ali Bango dan tsohon shugaban kasar ta Gabon ne Omar Bango.

'Yan adawar kasar ta Gabon dai na masu tababa da asalin shugaban kasar na Gabon na yanzu wanda suka ce asali dan kabilar Igbo ne ta Najeriya da tsohon shugaban kasar ya dauka riko a lokacin yakin Biafra.Wanda hakan ke nufin cewa bai halatta ya shugabanci kasar ba wacce kundin tsarin milkinta ya tanadi cewa sai mutuman da aka haifa a cikin kasar ta Gabon ne ke da hurumin shugabancin kasar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke shirin shiga zabuka a shekara ta 2016 inda 'yan adawar ke neman haramtawa Shugab Ali Bango damar sake tsayawa takara