1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tababa game da zaɓen shugabancin Mali

July 4, 2013

Bayan da kotun tsarin mulkin Mali ta amince da takarar mutane 28 a zaɓen shugaban ƙasa, shugaban hukumar zaɓen ƙasar ya bayyanawa shakku game da tsabtar zaben na 28 ga Yuli.

https://p.dw.com/p/192KY
Shirye-shiryen zabe sun kankama a MaliHoto: Reuters

Shugaban hukumar zaɓen Mamadou Diamoutani ya ce akwai kura-kurai da dama a tsarin zaɓen ƙasar da za su iya zama sanadiyyar murɗiyya. Kuma ya ce babban ƙalubalen da hukumar ke fuskanta yanzu, shi ne raba katin zaɓe ta yadda zai kai ga mutane kusan milliyan bakwai tsakannin makwanni huɗu, ganin cewa kusan dubu 800 daga cikinsu sun rasa matsugunnensu, wasu ma suna gudun hijira. Wata matsala kuma ita ce, mata aƙalla dubu 300 masu shekaru 18 zuwa 19 waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a bisa tanadin dokar ƙasar, ba za su iya zaɓe ba kasancewar an yi rejistar zaɓen ne tun a shekarar 2010 lokacin shekarunsu ba su kai ba.

Ana bukatar shaidar zama dan kasa kafin a yi zabe a Mali
Hoto: Sebastien RIEUSSEC/AFP/Getty Images

Rashin bin ka'idoji na wasu 'yan takara a Mali

Mutane 36 ne suka nemi tsayawa takarar muƙamin shugaban ƙasa amma 28 kaɗai ne suka ƙetara kamar yadda Yaya Konate, wakilin DW da ke Bamako ya bayyana cewa "Daga cikin 36 da suka nemi takarar, kotun tsarin mulkin ƙasar ta cire mutane takwas a hukuncin da ta yanke, waɗanda ta ce ba su cika ƙa'idojin da dokar zaɓen ƙasar ta tanadar ba. Haka nan kuma ba su sami adadin masu rufa masua bayan da ake buƙata ba"

A waje guda kuma, bayan furucin shugaban hukumar zaɓe kan tababar da yake yi na gudanar da zaɓe mai sahihanci, Jam'iyya mafi girma ta Malin ta kira wani taron gaggawa inda mai magana da yawunta Iba Ndiaye ya ce kamata ya yi gwamnati ta kira taro na musamman da su 'yan takara da jam'iyyunsu, domin fayyace dokokin zabe saboda su kaucewa ƙalubalen da akan fuskanta bayan zaɓe.

Daga cikin 'yan takara a Mal har da mace

Ko da shi ke 'yan takaran sun haɗa da jiga-jigan 'yan siyasan ƙasar kamar su Ibrahim Boubacar Keita shugaban RPM, Soumaila Cisse na Union de la Rebulique et la Democratie da kuma tsoffin firaminostocin ƙasar. Sai kuma sabbin fuskoki irinsu Moussa Mara Yelema magajin garin Oulessebougou da ke cikin Bamako da ma dai Haidara Aissata Cisse wacce 'yar majalisa ce daga yankin Gao . Wakilin DW Yaya Konate ya yi mana ƙarin bayani kan yanayin ƙasar bayan wannan sanarwa inda ya ce: "Bayan da aka wallafa waɗannan sunaye, jaridun ƙasar sun bayyana wannan shawarar da kotu ta yanke, inda 'yan ƙasa suka fara ƙoƙarin ganin fuskokin waɗannan mutane, a ɗaya daga cikin jaridun ma, ministan cikin gida ya ƙara tabbatar wa jama'a cewa za'a gudanar da zaɓen na ranar 28, amma kuma dangane da waɗanda suka nemi takarar shugaban ƙasa, idan har bayan sao'i 24 ba su ɗaukaka ƙara ba alƙalan kotun tsarin mulkin guda 9 za su sake bayyana 'yan takara 28 da suka amince da su tun farko a mataki na ƙarshe"

Wahlen in Mali
Shugaban rikon kwarya ba zai tsaya takara baHoto: DW/K. Gänsler

A yanzu haka dai, ana sa ran ɗage dokar ta ɓacin da ke kan yankunan ƙasar ta Mali a lahadi mai zuwa, ranar da ake sa ran ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe.

Rahoto cikin sauti na kasa

Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Mouhamadou Awal