April 2, 2019
Talla
Ranar 20 ga watan Maris na ko-wacce shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe a zaman ranar tuni da gatana ko tatsunniya. A bana dai ranar ta zo dai dai da lokacin da masu yawancin shekaru wato dattawa da suka hada da maza da mata wadanda suka girma a gaban kakanni suka kamu da kishirwar abokan hira a dandali, lamarin da ke ci gaba da sa su yin santin yadda suka zauna da kakaninsu a baya. A wannan makon cikin na TKL da ya ke duba batutuwan da suka shafi al'adu addinai da kuma zamantakewar al'umma za mu duba tasirin tatsuniya a rayuwar yanzu da ta da, musamman a janhuriyar Nijar