1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: Masarautar Tsibiri

Salissou Boukari
June 15, 2021

Shirin zai yada zongo ne a Jamhuriyar Nijar inda ya duba wasu shagulgulla na raya al’adun masarautar Tsibiri da ke cikin gundumar Dogon Doutchi a jihar Dosso.

https://p.dw.com/p/3uyCO
Niger Tuareg Marriage Hochzeit
Hoto: picture-alliance/dpa/D. von Trotha

A Jamhuriyar Nijar, an gunadar da shagulgullan ba da mukamai ga wasu 'yan sarautar Tsibiri a wani mataki na raya al’adu tare da daukaka martabar wannan masarauta mai babban tarihi, masarauta ce da ke da alaka da masarautar Daura a Najeriya da kuma babbar alaka da Sarauniya ta Lungu.

Sarki na farko da ya yi gwagwarmaya a wannan kasa ta Tsibiri shi ne Mai Martaba Samna Karfe Tounkara, wanda aka haifa a wajejen 1807 sama da shekaru 200 kenan da suka gabata. Kuma sarki ne da ya yi kokowar kwato wa al’ummarsa da sauran yankin 'yancinsu daga wasu saraki da a wancan lokaci ke muzgunawa al’umominsa ta hanyar biyan haraji da dai sauransu, inda tare da wasu sarakuna da suka mara masa baya suka yi nasarar kwato yancin shekaru 200 da suka gabata tun a lokacin daular Usmaniya.

Kuma kasar Tibiri da ke yankin Arewa, ta samu sarakuna har guda 12. A cikin shirin Alou Mamane daya daga cikin yayan wannan masarauta ya bayyana jerin sunayen wadannan sarakuna har ya zuwa mai ci yanzu. 

MMT-Kultur & Gesellschaft (16.+17.6.21) - MP3-Stereo