Taba ka Lashe: Baje kolin kayan sarautar Damagaram | Zamantakewa | DW | 29.01.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Taba ka Lashe: Baje kolin kayan sarautar Damagaram

Muhimman hotunan Hawan Daushe na wasu daga cikin fadawan sarkin Damagaram na shekarar 1900 gami da kayan tarihin masarautar kimanin guda 80 aka baje kolinsu baya ga saura.

A kwanakin baya ne a birnin Damagaram na Jamhuriyar Nijar masarautar birnin ce da hadin gwiwar gidan raya al'adun gargajiyar Faransa da Nijar wato CCFN suka bude baje kolin kayan tarihin masarautar tun na shekarar 1900. Wannan ko ya zo dai dai da lokacin da shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron ya ambata cewar Faransa na maida wa kasashen Afirka kayansu na tarihi a yayin wata ziyara da ya kai kasar Burkina Faso a kwanakin baya.

Kafin dai bude bajekolin mai alfarma sultan na Damagaram Aboubacar Oumarou Sanda ya yi matashiya game da bikin baje kolin kayan tarihin na masarautar Damagaram.

Muhimman hotunan Hawan Daushe na wasu daga cikin fadawan sarkin Damagaram na shekarar 1900 gami da kayan tarihin masarautar kimanin guda 80 aka baje kolinsu a dandamalin fadar masarautar da kuma gidan raya al'adun gargajiyar kasar Faransa da Nijar wato CCFN tare da tallafin Dr. Kamiy Lefèbre daya daga cikin kwararrun Turawan Faransa masu bincike wacce ta lakanci tarihin Damagaram. Kamiy Lefebre ta ba da kadan daga cikin dalilan da suka sa aka mayar wa Damagaram kayan tarihinta.

Saurari sauti 09:45

Taba ka Lashe: Baje kolin kayan sarautar Damagaram

"Mun bukaci kawo su nan don bai wa mutanen gari damar ganinsu. Kusan hotuna dari ne, wadanda ake iya samunsu a nan ko a cibiyar yada harshen Faransanci da ke bayani kan tarihin Zinder. An dauki hotunan farko a shekarar 1899.Abin da yake daukar hankali shi ne halin da Damagaram ke ciki a karnin na 19 a fannin kasuwanci da tsarin sarauta, ma'ana duka 'yan kasuwa da masana na wancan lokaci da suke kara wa garin kima a yankin baki daya."

Masaniyar kuma mai binciken tarihin Damagaram ta kara da yin takaitaccen tarihin ginin masarautar ta Damagaram; Don jin karin bayani sai a latsa shirin na saurare.

 

Sauti da bidiyo akan labarin