1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 24.01.2018

Mohammad Nasiru Awal
January 26, 2018

Abubakar Adam Ibrahim marubuci daga arewacin Najeriya a watannin baya bayan nan ya samu damar zuwa tsibirin Sylt na 'yan yawon shakatawa da ke arewacin Jamus, inda ya karasa wani littafi da yake rubutawa.

https://p.dw.com/p/2ra3t

Shi dai Abubakar Adam Ibrahim an haifeshi ne a shekarar 1979 a garin Jos da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, marubuci ne na gajajjerun labarai, amma ya fara samun shahara a duniya bayan wani cikakken littafinsa na farko da ya wallafa a 2016 mai suna "Season of Crimeson Blossoms", wanda kuma ya samu lambar yabo ta marubuta adabi a Najeriya a 2016.