1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 18.07.2018

Mohammad Nasiru Awal
July 19, 2018

Makaranta da ake kira ReDi da ke birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus ta kuduri aniyar hanzarta shigar da bakin cikin rayuwar yau da kullum a Jamus.

https://p.dw.com/p/31lV6

Daruruwa dubbai na 'yan gudun hijira ne suka shigo Jamus a shekara ta 2015, akasarinsu na shan gwagwarmayar don sajewa da 'yan kasa. Gaba daya dai sabbin zuwa na daukar tsawon lokaci har zuwa shekaru bakwai wajen koyan Jamusanci da tsayawa kan kafafunsu da ma neman aiki a kasar. Wata makaranta da ake kira ReDi da ke birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus ta kuduri aniyar hanzarta shigar da bakin cikin rayuwar yau da kullum a Jamus.