Taba Ka Lashe: 09.+10.03.2016 | Al′adu | DW | 13.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Al'adu

Taba Ka Lashe: 09.+10.03.2016

Tashar Refugee Radio Network ta 'yan gudun hijirar ke watsa shirye-shirye ga takwarorinsu 'yan gudun hijira.

A bara kawai 'yan gudun hijiran fiye da miliyan daya ne suka shigo Jamus neman mafaka, sannan a kullum wasu na kara shigowa kasar, suna jiran a yi rajistar sunayensu a cibiyoyin da aka tanadar musamman don karbar sabbin bakin. Akasari wadannan 'yan gudun hijira ba su iya harshen Jamusanci ba, saboda haka suna shan wahala wajen samun gamsassun labarai da bayanai. Sai dai wasu mutane a birnin Hamburg da ke arewacin Jamus sun tashi haikan don kawo canji, inda suka kafa tashar Refugee Radio Network ta 'yan gudun hijirar ke watsa shirye-shirye ga takwarorinsu 'yan gudun hijira.

Sauti da bidiyo akan labarin