Ta′addanci: Jigon yakin neman zabe a Birtaniya | BATUTUWA | DW | 07.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Ta'addanci: Jigon yakin neman zabe a Birtaniya

Birtaniya za ta gudanar da babban zabe a wannan Alhamis, inda sakamakon hare-haren ta'addanci da kasar ta fuskanta kwanakin nan, batun tsaro ya mamaye yakin neman zaben.

Yayin da kasar Birtaniya za ta gudanar da babban zaben ta, batun tsaro ya mamaye yakin neman zaben. Haka nan ma akwai batun dangantakar kasar da sauran kasashen da ke nahiyar Turai. 

Bayan kasar Faransa, a bayyane ya ke cewar a Birtaniyar ma hare-haren ta'addanci da suka auku a biranen Manschester da London sun mamaye harkokin zaben. Kasar ta kadu kuma jam'iyyun siyasa sun amince suka katse yakin neman zabe bayan harin gadar London Bridge a karshen mako. Harin ta'addancin baya-bayan nan da aka kai birnin London ya kara karfafa takaddama da ta dabaibaye Firaminista Theresa May ta jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya ta Conservative da mai kalubalantarta Jeremy Corbyn na jam'iyyar Labour.

Ko da yake bayan harin na ranar Lahadi May ta lashi takobin daukar matakan ba sani ba sabo kan 'yan ta'adda, amma a cewar Anthony Glees masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Buckingham tarihinta a matsayin sakatariyar harkokin cikin gida ya zame mata alakakai.

Ya ce: "Mun san cewa akwai mutane kimanin dubu 23 da ake zargi 'yan Jihadi ne a Birtaniya, amma ba za a mu iya sanya ido kansu ba, domin Firaminista Theresa May a lokacin da take sakatariyar harkokin cikin gida shekarar 2010 ta soke aikin sa idon.

Shi ma Jeremy Corbyn na babbar jam'iyyar adawa ta Labour ba samu wani tagomashi ba bayan harin, inda banda kiran da ya yi wa Firaministan ta yi murabus, inji Glees.

Ya ce: "Jam'iyyar Labour karkashin jagorancin Jeremy Corbyn, wanda ke nuna zumunci da kungiyar IRA ta lardin Ireland ta Arewa, jam'iyyarsa ta nuna adawa da umarnin harbi da tattaunawa da 'yan ta'adda a lokacin kamfen."

 

Inda hankalin 'yan takara ya karkata

Batun tsaron dai shi ne ya mamaye rana ta karshe a yakin neman zaben, inda Firaminista May ta yi alkawarin murkushe tsattsauran ra'ayi idan ta lashe zabe ko da hakan na nufin take dokokin kare hakkin dan Adam ne.

Ta ce: "Dauri shekaru da yawa ga wadanda suka aika laifin ta'addanci, saukaka iza keyar baki 'yan ta'adda kasashensu na asali. Za mu kara azama wajen takaita 'yanci da walwalar wadanda ake zargi da ta'adda. Idan dokokin kare dan Adam za su kawo mana tarnaki, za ju canja su."

Kommunalwahl in England Boris Johnson (picture-alliance / dpa)

Sai dai a martanin da ya mayar shugaban Labour Jeremy Corbyn ya ce watsi da dokokin demokardiyya ba shi ne mafita ba a kokarin tabbatar da karin tsaro a Birtaniya.

Ya ce: "Ya kamata mu kare 'yancinmu da demokardiyya da kuma hakkin dan Adam. Mun sanya hannu kan kudurin Turai na kare hakkin dan Adam. Dokarmu ta kare mana 'yancinmu. Rage tsarin demokradiyya ba shi ne hanyar tinkarar bazaranar da demokardiyya ke fuskanta ba. Dole mu tinkari barazanar kanta."

Kasar Birtaniya dai na fama da rarrabuwar kawuna, 'yan siyasa sun kasa yin wani katabus domin kasar na cikin mawuyacin hali, tun a bara al'umarta ta kada kuri'ar ficewa daga tarayyar Turai wato Brexit, amma har yanzu suna jiran a yi musu bayani ainihin abin da Brexit din ke nufi.

Sauti da bidiyo akan labarin