Ta′addanci a Najeriya da rigingimu a Mali | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 14.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Ta'addanci a Najeriya da rigingimu a Mali

Ayyukan tarzoma a Najeriya da rashin sanin tabbas a kasar Mali duk da yarjejeniyar zaman lafiya na daga cikin batutuwan nahiyar Afirka da suka dauki hankali jaridun Jamus a wannan mako.

Ayyukan tarzoma a Najeriya da rashin sanin tabbas a kasar Mali duk da yarjejeniyar zaman lafiya na daga cikin batutuwan nahiyar Afirka da suka dauki hankali jaridun Jamus a wannan mako.

A labarinta mai taken mataki na gaba na yaki jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce jerin hare-hare ba su lafa ba a Najeriya, inda a wannan makon kasuwar Sabon Gari da ke a jihar Borno ta kasance wurin da Boko Haram ta kai mummunan hari, inda ta kashe mutane masu yawa sannan da dama suka jikkata.

Jaridar ta kara da cewa tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan karagar mulkin Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu yawan mutanen da hare-haren ta'addanci ke shafa ya karu duk da nasarar da rundunar hadin guiwa ta kasashen Najeriya, Nijar Kamaru da Chadi ke samun a kan 'yan tarzomar.

A ranar Laraba ma dai Shugaban Chadi Idris Deby ya ce kungiyar Boko Haram ta samu sabon jagora mai suna Mahamat Daoud da ya nuna shirin shiga tattaunawa da gwamnatin Najeriya. Sai dai jaridar ta ce bai kamata a dauki kalaman na Deby da muhammanci ba.

Rashin tabbas a kasar Mali

Daga rikicin Boko Haram a Najeriya sai na wani rikicin a Mali inda a cewar jaridar Neue Zürcher Zeitung duk da wata yarjejeniyar zaman lafiya, har yanzu kasar da ke a yankin Sahel na fama da halin rashin tabbas.

Mali Anschlag Hotel Byblos

Wani daki a otel din Byblos da aka kai wa hari a Mali

A ranar Talata wata kungiya da kawo yanzu ba a santa ba ta dauki alhakin mummunan harin ta'addanci da aka kai kan wani otel a Mali karshen mako da ya hallaka mutane 13 ciki har da ma'aikatan Majalisar dinkin Duniya su biyar. Wani mai ikirarin jihadi da ya kira kansa Suleiman Mohammed ya fada wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa kungiyarsa ta Mujahedin ta kai hari a otel din da ma wanda aka kai ranar Litinin kan wani sansanin sojojin gwamnati da ke tsakiyar kasar. An shiga wannan yanayi ne bayan da a cikin watan Yuni aka samun kwarin guuwar yin kyakkyawan fata biyo bayan sanya hannu kan wata yarjejeniyar ba wa yankunan Timbuktu da Kidal da kuma Gao karin 'yancin cin gashin kai tare da basu kaso mai tsoka na kudaden kasa.

Shugaban leken asirin Ruwanda ya samu kanshi

An sako shugaban hukumar leken asirin kasar Ruwanda inji jaridar Die Tageszeitung, inda ta kara da cewa hukumomin shari'a a kasar Birtaniya sun yi watsi da shari'ar da ake wa Karenzi Karake na aikata laifin yaki.

Ruanda Sicherheitschef Karenzi Karake

Karenzi Karake shugaban hukumar leken asirin Ruwanda

Jaridar ta ce bayan ya shafe wata daya da rabi a gidan wakafin na Birtanyia yana jiran a mika shi ga hukumonmin kasar Spain, a ranar Litinin da ta gabata wani alkali a birnin London ya sako Janar Karenzi Karake, bisa shawarar lauyoyin gwanati. A ranar 20 ga watan Yuni aka cafke Janar din a filin jirgin saman Heathrow na birnin London lokacin da yake shirin tashi zuwa Ruwanda bayan wani hutu da ya yi a London. Sunansa na cikin jerin sunayen manyan jami'an Ruwanda 39 da masu shigar da kara na kasar Spain suka ba da sammacin kamesu a shekarar 2008. Ana zarginsu da hannu a kisan kiyashin da ya auku a Ruwanda a 1994.