Taaddanci a jamus | Labarai | DW | 08.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taaddanci a jamus

Rahotanni na nuni dacewa mutanen nan uku da aka cafke bisa zargin shirin kai harin tarzoma a wasu sassan nan jamus,nada umurnin kai wadannan hare hare kafin ranar 15 ga wannan wata na Satumba ,kuma suna sane dacewa ynasanda na lura da lamuransu ,kafin cafkesu da akayi a ranar talatar data gabata.Wani rahotan da mujallar Der Spiegel dake nan jamus ta gabatar na nuni dacewa,an bawa mutanen uku waadin makonni 2 na aiwatar da wadannan hare haren,a wata kira da suka samu ta wayan tangaraho daga yankin arewacin kasar Pakistan,wanda jamian yansandan jamus din suka saurara tun a karshen watan Augustan daya gabata.Wannan shirin kai harin dai ya tarwatse,lokacin da yansanda suka cafke wadannan jamusawa guda 2 da suka musulunta da baturke guda.