Ta fadi gasassa ga APC a majalisa | Siyasa | DW | 27.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ta fadi gasassa ga APC a majalisa

Jam'iyyar adawa ta APC a Tarayyar Najeriya ta ce ta farauto kimanin 'yan majalisar wakilai 50 daga jam'iyyar PDP mai mulki a kasar da nufin sauya musu sheka zuwa APC.

Duk da cewar dai har ya zuwa yanzu babu batun na sauyin sheka a cikin zaurukan majalisun Najeriya gudar biyu, amma kuma daga dukkan alamu an kai nesa ga batun sauyin sheka a tsakanin 'ya'yan majalisun kasar biyu da suka kai ga biyo baya ga matakan gwamnonin jamiyyar biyar na sabuwar PDP. Honarable Bashir Baballe dai na zaman dan majalisar wakilan kasar daga jihar Kano kuma daya daga cikin masu sauyin sheka daga PDP ya zuwa APC, a fadar sa babu gudu babu ja da baya bisa matakin da yace na da kariyar kundin tsarin mulkin kasar dama dokokinta.

Ya ce "Da yawa daga cikin 'yan sabuwar PDP mun shiga sabuwar jam'iyyar APC, domin in zaka iya tunawa sati hudun da suka wuce shuugabannin jam'iyyar APC sunje sun zauna da shugabanninmu wanda muma an tuntubemu, kuma muka ce zamu tuntubi jama'armu, bayan mun tuntubesu a bin da muka ga mafita shine mu shiga ita jam'iyyar APC. Wato a kullum ana tsorata mutane da kujeru, tsarin mulki ne ya kawo mu nan kuma shine zai iya fidda mu, babu wani shugaban jam'iyya da ya isa yace mun rasa kujerunmu, abin da tsarin mulki ya ce shine zaka iya rasa kujeraraka idan kana cikin wata jam'iyya kazo ka fita, amma a karshe sai ya ce idan da rikici a jam'iyarka zaka iya fita ko kuma idan jam'iyyarka ta fita ta hada gwiwa da wata".

General a.D. Muhammad Buhari

General Muhammad Buhari jagoran jam'iyyar adawa ta APC dake tsintar dami a kala.

Ficewar sababbin 'yan PDP dai na nufin kama hanyar rikidewar majalisar wakilan kasar zuwa ga mai rinjayen APC abun kuma dake iya kafa sabon tarihi na siyasa dama kila tabbatar da sauyin rawar siyasa a kasar. Dama dai an dauki lokaci ana kallon kawance a tsakanin 'yan adawar da 'yan tawayen dake juya akalar majlisar kasar da a baya sukai nasarar hana PDP rawar gaban hantsi a zaurukan da rinjayen kusan kaso 70 cikin 100. Honarrable Abdul-Rahman Kawu Sumaila dai na zaman mataimakin shugaban masu adawar APC a cikin majalisar wakilan kasar ta Nijeriya, a cewarsa a shirye suke da nufin taka sabuwar rawa a cikin tsarin da ya kama hanyar daidaita yawansu da 'yan jam'iyyar PDP mai mulki.

Yace:Abin sha'awa shine duk kanin manyan jihohin Najeriya suna hannun adawa yanzu, Legas da Rivers da Imo da Kano da Borno da kuma Sokoto, dukkaninsu suna hannun 'yan adawa yanzu. Don haka abin da zan iya cewa shine Alhamdulillahi yanzu siyasar za ta yi dai za a girmama siyasa, za a girmama 'yan siyasa, za kuma a girmama 'yan kasa".

Rabiu Musa Kwankwaso

Daya daga cikin gwamnonin da suka yiwa jam'iyyar PDP tawaye Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano.

To sai dai koma wane irin sauyi ake shirin gani a zauren majalisun kasar ta Najeriya biyu, daga dukkan alamu suma dai masu tunanin sai PDP har Mahadi na shirin ganin kare muradun jamiyyar tasu ko ana ha maza ha mata a fadar Honarrable Jagaba Adamas Jagaba da yace wai ko in kula in ji ungulun da ta taka mushen mota.

Yace:"Matsayin PDP ya kai inda duk taruwar mutane ba zai ka da PDP ba, sai dai kawai Allah ya kata ita. Suma 'yan APC din da suka koma suka samesu, wato kamar taruwar kuda ne a kan fata. Domin ko kawo kuda miliyan daya ka zuba a kan fatar Sa, zai ta lashe jinin amma ba zai iya huda fatar ba. To taruwar 'yan PDP a APC ba zai taba kada PDP ba".

Abin jira a gani dai na zaman mafita a cikin sabon yanayin da nan da 'yan kwanakin dake tafe, ke iya kaiwa ga zama fitilar inda siyasar kasar ta kama hanyar fuskanta.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Mouhamadou Auwal Balarabe/LMJ

Sauti da bidiyo akan labarin