Taɓa Ka Lashe: 30.12.2009 | Al′adu | DW | 06.01.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Al'adu

Taɓa Ka Lashe: 30.12.2009

Bikin na bana dai shi ne karo na 40, wanda kuma ya zo daidai da cikar shekaru bakwai da hawa kan karagar mulki na mai martaba Mohammadu Hayatu Hamadina

A ƙasar Kamaru a tsakiyar makon da ya gabata ne al´umar Yem-Yem dake garin Galim-Tignère suka kammala bikin da suke gudanarwa kowace shekara. Bukukuwan da aka kwashe tsawon kwanaki uku ana yi, ya kasance na nuna murna da jinjinawa sarakunansu na gargajiya na zamanin da waɗanda suka kuɓutar da su daga hannun turawan mulkin mallaka na ƙasar Jamus.

Bikin na bana dai shi ne karo na 40, wanda kuma ya zo daidai da cikar shekaru bakwai da hawa kan karagar mulki na mai martaba Mohammadu Hayatu Hamadina.

Sarakunan gargajiya na ciki da wajen Kamaru da suka haɗa da na ƙasashen Najeriya da Chadi na daga cikin manyan baƙi da suka halarci wurin bikin na bana.

Sauti da bidiyo akan labarin