Taƙaddamar shige da fice tsakanin Libiya da Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) | Labarai | DW | 28.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taƙaddamar shige da fice tsakanin Libiya da Ƙungiyar Tarayyar Turai(EU)

An kawo ƙarshen taƙaddama tsakanin Libiya da Ƙungiyar Tarayyar Turai.

default

Nikolas Sarkozy da Angela Markel yayin shawarwarin EU

An kawo ƙarshen taƙaddamar da ke tsakanin Libya da kuma ƙungiyar Tarayyar Turai(EU) game da haramcin da Tripoli ta ƙaƙaba wa Turawan ƙasashen na shiga Libya. An kawo ƙarshen wannan mataki ne dai bayan da EU ta ɗage haramcin shiga ƙasashen Turai da ƙasar Switzereland ta sanya wa wasu 'yan ƙasar Libiya 200 bayan wani rikici da ya kunno kai tsakanin Switzerland da Libiya a shekarar 2008. Sai dai kuma duk da wannan mataki da aka ɗauka Ministan harkokin wajen Libiya, Mussa Kussa, ya sheda wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, har yanzu akwai sauran rina a kaba game da rikicinta da ƙasar Switzerland. A cewar Ministan dole a gudanar da wata shari'a tsakanin ƙasashen biyu, don gane matakan da Switzerland ta ɗauka akan Libiya a shekarar 2008. A wancan lokaci dai Switzerland ta tsare ɗan shugaba Ghaddafi ne, bisa zargin da ake masa na gallaza wa wasu masu masa hidima a wani Otel da ke birnin Geneva. Yanzu haka dai akwai wani ɗan kasuwar Switzerland, Max Goeldi, wanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin watannin huɗu a gidan yarin Libiya, bayan dakatar da cinikin man fetur da rufe Asusun ajiyan ƙasar ta Libiya a Bankunan Switzerland. Wannan ya sa gwamnatin Switzerland ta ƙaƙaba takunkumin shiga ƙasar ga wasu 'yan Libiyan kimanin 188 da suka haɗa da shi kansa shugaba Kadhafi da iyalansa. Ƙasar Spain da ke riƙe da ragamar shugabancin karɓa-karɓa na EU ne dai ta taimaka wajen ɗage wannan haramci.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Halima Abbas