Taƙaddamar China da Japan a kan tsibirin Senkaku | Labarai | DW | 04.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taƙaddamar China da Japan a kan tsibirin Senkaku

Mataimakin shugaban Amirka Joe Biden na ƙoƙarin neman shiga tsakani a rikicin da China ta ke yi da sauran ƙasashen yankin Asiya.

Mataimakin shugaban Amirka Joe Biden ya isa a China inda zai gana da shugabannin ƙasar,domin tattauna rikicin da ake yi tsakanin China da Japan.

Dangane da shata wani sabon zango na sararrin samaniya a tekun Chinar a kan tsibiri Senkaku Diaoyu wanda ake yin taƙaddama a kansa tsakanin China da Japon wanda su dukkanisu ke ikirarin cewar mallakarsu ne. Joe Biden wanda ya taso daga Japan a rangandi da ya ke ci gaba da yi a yanki Asiyar, zai tashi gobe daga China zuwa birnin Seoul na Koriya ta Kudu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
dita : Umaru Aliyu