Taƙaddama tsakanin China da Japan | Labarai | DW | 13.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taƙaddama tsakanin China da Japan

Ƙasashen biyu na ci gaba da yin takun saƙa a kan tsibirin Senkaku wanda ko wane daga cikin ɓangarorin ke yin iƙirarin cewar mallakarsa ne

Rikici tsakanin ƙasar China da Japan a kan tsibirin Senkaku, ya ƙara zafafa,bayan da Japan ta sanar da cewar wani jirgin sama bincikke na yaƙi na ƙasar ta China ya keta sararin samaniyarta a karon farkon tun da ricikin ya rincaɓe a cikin watan Satumbar da ya gabata,a lokacin da wani ɓangaran tsibirin ya zama mallakar Japan.

Kakkakin gamnatin ta Japon Osamu Fujimura ya ce sun aike da jiragen yaƙi guda fudu a sansani ,sai dai ya ce babu wata karawa da aka yi tsakanin jiragen na ƙasashen biyu.China ta buƙaci Japan da ta dai'na, gudanar da harkokin a cikin ruwayen da sararin samaniyar tsbirin na Diayou wanda ta ce mallakarta ne.Wannan al'amari ya faru ne a sa'ilin da ƙasar China ke gudanar da bukukuwan nuna juyayi na zagayowar cikkar shekaru 75 da aikata kisan kiasun da Japan ta yi a kan yan China a garin Nankin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abass