Taƙaddama kan tsadar farashin wutar lantarki | Siyasa | DW | 16.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taƙaddama kan tsadar farashin wutar lantarki

Bayan alƙawuran da mahukuntan Najeriya suka yi na kyautata al'amuran da suka shafi wutar lantarki, kawo yanzu babu biyan buƙata, amma kuma an ƙara farashi fiye da kima

Wata taƙadamma ta kunno kai a tsakanin gwamnatin Najeriya da ƙungiyar ƙwadagon ƙasar a agame da ƙarin farashin kuɗin wutar lantarki wanda kungiyar tace ba za ta lamunta ba, domin kuwa mataki ne na jefa talakan ƙasar cikin sabbin wahalhalu.

Ƙarain kuɗin wutar lantarki da hukumar kula da harkokin wutar lantarkin Najeriya ta sanar, wanda ya sanya farashin wutar tashin gwauron zabi daga Naira 225 zuwa Naira 700 kowane unit na wuta, ya sanya ƙungiyar ƙwadagon Najeriyar yin watsi da ƙarin bisa cewa ba abu ne da ba za ta lamunta ba.

Duk da cewa wannan ƙari ne da hukumar ta saba yi duk shekara a Najeriya, to sai dai a wannan lokaci an yi ƙarin da ya zarta kashi 50 cikin ɗari a dai dai lokacin da ake ci gaba da fuskantar katsewar wutar lantarki a cikin kasar, duk kuwa da alƙawarin da gwamnati ta daɗe tana yi na samun ingantuwar wutar. Comrade Abbayo Nuhu Toro shi ne sakatren kula da harkokin ma'aikata da haƙƙoƙinsu na ƙungiyar ƙwadagon Najeriyar, ya bayyana dalilan ya sanya su watsi da wannan kari.

Farashin wutar lantarkin

"Abin takaicin shi ne kaman ana yaudarar jama'a ne, wutar lantarkin nan babu ita, in da a ce akwai wutar lantarkin in aka ce za a ƙara kuɗi ba wanda zai yi Magana, to amma kaman saye da sayarwa ne a kasuwa, kana sayar da abu babu shi, kuma ka ce zaka ƙara kuɗi ya zama zalunci. Saboda haka muka ga ya dace shugaban Najeriya ya hanzarta tilastawa waɗanan ma'aikatun da aka baiwa haƙin ƙarawa da rage farashin wutar lantarki, su gaggauta maida farashin a kan Naira 225. Saboda haka muddin basu mayar da kuɗin wutan ba to ƙungiyar ƙwadago za ta ɗauki mataki a kansu"

Bisa koken da ƙungiyar ƙwadagon ke yi na tsadar da wuta lantarkin ke ƙara yi a Najeriya duk da rashin wadatarta da ke jefa alumma a yanayi na a doke ka a hana ka kuka to amma Dr Sam Amadi shugaban hukumar kula da harkokin kamfanonin wuta lantarkin Najeriya yace akwai matakai da aka dauka don sauƙaƙawa masu ƙaramin ƙarfi.

"Abin da yafi damunmu shi ne mu tabbatar da cewa farashin wutar lantarki da aka sa ya baiwa masu zuba jarri dammar su samo maida jarrin da suka zuba, to amma duk da haka mun tsara farashin wutan lantarki wanda zai zama mai inganci kuma jama'a zasu iya saye, don haka ne muka karkasa yadda jama'a zasu biya kudin ya bambanta daga kamfanonin zuwa masu ƙaramin ƙarfi, sanan mun sanya tallafin da gwamnati ke bayarwa a cikin lamarin don rage raɗɗaɗin farashi ga talaka. Duk wannan don mu tabbatar da farashin ya kasance mai sauki sosai"

Matsayin Ƙungiyar Ƙwadagon Najeriya

Ƙungiyar ƙwadagon Najeriyar da ke shirin kwasan yan kallo da gwamnati a kan ƙarin ƙudin wutar a cikin ƙasar na bayyana cewa sabon farashin ba abinda talakan Najeriya zai iya biya bane, musamman bisa la'akari da ƙarin da za a kwashe shekaru 15 ana aiwatarwa, abin da ke nuna cewa bai wuce kashi goma na 'yan Najeriya ne zasu iya samun karfin biyan kudin ba. To ko wane mataki suke shirin ɗauka? Har ila yau ga Comrade Abbayo Toro

"Batun samar da wutar lantarki da ma ƙarin farashinta dai lamari ne da ke cike da sarƙaƙiya a Najeriya, musamman bias la'akari da maƙudan kuɗaɗen da ake ci gaba da kashewa a wannan fani ba tare da ganin sahihin ci gaba ba, saboda har wannan lokaci yawaitar katsewr wutar latarki na ci gaba da zama babu birni ba ƙauye."

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin