Taƙaddama kan Iran | Siyasa | DW | 20.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taƙaddama kan Iran

An samu martani mai tsauri daga ƙasashen Turkiya da Burazil kan ƙudurin da aka zartar, na sake azawa Iran ƙarin takunkumi

default

Erdogan da Ahmadinejad

Ƙasashen Burazil da Turkiya sun gargaɗi kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya bisa sabbin takunkumi kan ƙasar Iran. Inda suka ƙira ƙasashen 15 dake da wakilci a kwamitin sulhu da su, bada damar ci gaba da tattaunawa. ƙasar Jamus da mammaben majalsar na dinduin biyar suna tsara wani daftari, da za'ayi aiki da shi, amma masana na cewa ba lallai bane ƙuduri ya kai ga dunfar da ƙasar Iran kan manufar ta mallakar nukiliya.

Sabon ƙudurin da ƙasar Amirka da gawayen ta suka yi kan ƙasar ta Iran, a dai dai lokacin da ƙasashen Turkiya da Burazil suka shawo kan Iran, inda ta amince da aikawa da uranium ɗin ta a sarrafa mata shi a wata ƙasa ta waje, ya sa ƙasar Turkiya ta fusata ainun. Inda ministan harkokin wajen ƙasar ta Turkiya yace wannan a fili yake ƙasashen yamma, sun saɓa amanar dake tsakaninsu. Don haka yace da kamata ya yi ayi anfani da ɗan bada kai da ƙasar Iran ta nuna.

Idan yanzu aka fara batun wani sabon takunkumi. To ina ma dalilin ɓata lokacin da mukayi, muna neman sasantawa? don haka muna ƙiran dukkan bangarorin, da su mutunta nauyin da ke kansu"

A fili take gwamnatin Turkiya dai ta nuna rashin jin daɗinta. Inda Firimiyan ƙasar Tayyib Erdogan yace, kowa gane da cewa, a fili take ƙasashen dake da ƙarfin faɗa ajia suna tafiyar da batun ƙasar Iran da wata manufa ta daban. Kana yace biyan buƙatunsu ne kawai suka sa a gaba.

Idan waɗannan ƙasashen za su iya mallakar makaman ƙare dangi, amma suce sauran ƙasashe basu da yancin mallakar su, kana ayi ta musu barazana, to ina gaskiya take. A gaskiya akwai ayar tambaya da yakamata mu yi.cin za mu kare ƙasashe masu ƙarfin faɗa ajine, ko kuma dokoki da tsarin duniya yakamata mu kare. Waɗan nan tambayoyi dole ne mu samu amsarsu"

Gwamnatin ƙasar Iran martanin ta kan sabon takunkumin ba mai tsauri bane. Wakilin ƙasar Iran a hukumar hana yaɗuwar makam uranium Ali Akbar Salehi, yace in dai ƙasashen da ake giran ƙasa da ƙasan, Amirka ce da ƙawayen ta, to suje, babu wani sabon abinda zai faru, haka batun zai sukulkulci, kamar na baya. Shi kuwa Ministan harkokin wajen Iran Munashir Muttaƙi, ƙarawa ya yi da cewa, a hasacensa wannan ƙudurin da ƙasashen yamma suka tsara, ba zai samu karɓuwa ba a kwamitin sulhu na majalisar Ɗinkin Duiniya.

Yanzu dai abun jira shine ko Amirka za ta samu rinjayen da take buƙata a kwamitin sulhun. Manyan ƙasahen yamma dai za su goyi bayan Amirka, amma Turkiya da Burazil da ƙawayensu, za su ƙaurace. Ƙudurin dai ya buƙaci da a hanawa jami'an ruddunar juyin juya halin jamhuriyar ta musulci da sauran jam'an tsaro na ƙasar fita ƙetare.

Mawallafi: Usman Shehu Usman da Ulrich Pick

Edita: Umaru Aliyu