Taƙaddama bayan zaɓen gwamna a jihar Anambra | Siyasa | DW | 18.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taƙaddama bayan zaɓen gwamna a jihar Anambra

Bayan kammala zaɓen gwamnan jihar Anambra tana shirin barin baya da ƙura tsakanin hukumar INEC da 'yan adawa waɗanda su ka ce ba su yarda da tsarin zaɓen ba.

An dai share tsawon watanni kusan shida ana shiri ana kuma jibge jami'an tsaron da babu irinsu, to sai dai kuma an ƙare a cikin ruɗani a jihar Anambra inda yanzu haka zaɓen gwamnan jihar ke shirin barin baya da ƙura tun bai nisa ba.Duk da cewar dai jam'iyyar APGA da ke mulki a jihar dai ce ke kan gaba da ƙuri'u sama da 174,000, sakamakon zaɓen dai ya gaza kammala a ɓangren hukumar zaɓen da ta ce har yanzu da sauran gyara kuma ke shirin saka wata ranar kammala sassan da ta ke ganin da sauran aiki a cikinsu. Ra'ayi dai ya banbanta tsakanin hukumar da ta ce tana shirin sake zaɓen ne a rumfunan da ke fuskantar rikici, da kuma manyan jam'iyyu uku masu adawa da ke cewar sake ɗaukacin zaɓen na zaman mafita na ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da adalci a cikinsa.

Zaɓen na Anambra da ake yiwa kallon zakaran gwajin dafi ga ƙoƙarin hukumar zaɓen na shirya zaɓuka masu karɓuwa a shekara ta 2015 dai tuni ya fara jawo ɗar-ɗar a tsakanin 'yan siyasa dama masu kallon baƙin hadari na siyasar rikici a gaba. Ga Tarrayar Najeriyar da ta fuskanci mummunan rikicin da yai barazanar ganin bayanta a shekara ta 2011, sannan kuma ake yiwa kallon dan ba na tashe tashen hankulan da suka mamaye ɗaukacin ƙasar ya zuwa yanzu.Tuni dai aka fara kiran karatu na gazawa ga jami'an hukumar zaɓen da suka kai ga kisa na maƙudai na kuɗi ba tare da kai wa ga kwantar da hankula cikin jiha ɗaya tilo ba, abun kuma da a faɗar dr Umar Ardo da ke nazari bisa harkoki na siyasa ke tabbatar da irin halayya ta mutanen da ke jagorantar ayyukan hukumar yanzu haka.

General a.D. Muhammad Buhari

Janar mai ritaya Muhammad Buhari na jam'iyyar adawa ta APC

Adalaci a cikin alƙalanci ko kuma son zuciya da cika ɓuri na siyasa dai daga dukkan alamu Tarrayar Najeriya na tsakanin tabbatar da zaɓe mai adalci ko kuma fuskantar ruɗanin da ke iya mummunar illa ga ɗaukacin fagen siaysar ƙasar. Abun kuma da ya kai ga mahukuntan ƙasar a matakai daban-daban jerin alkawuran darma sa'a da nufin bai wa maras'da kunya yayin zaɓukan da tuni suka kama hanyar raba kan yan ƙasar tsakanin addini da ƙabila. To sai dai kuma a faɗar Buba Galadima da ke zaman jigon jam'iyyar APC matsalar ta Anambra na zaman buɗe ido a garesu na sabon shiri da nufin tInkarar sabon ƙalubalen da ƙasar ta Najeriya ke shirin fuskanta a siyasance. To sai dai kuma in tai ɗaci ta kuma lalace ga masu adawa a Anambra ga 'yar uwarsu ta APGA da ta kama hanyar sake ɗare mulki a jihar wai duk wani ƙorafi na 'yan adawa bai wuci bakin masu shirin rasa damar mulki ba a faɗar Sani Abdullahi Shinkafi da ke zaman sakataren jam'iyyar na ƙasa .Abun jira a gani dai na zaman mafitar rikicin da ma matakai na gaba a ɓangaren hukumar zaɓen da ke ƙara fuskantar fushi da ba daɗi na 'yan ƙasar a kullu yaumin.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin